Fit 31
31
Waɗanda za su Yi alfarwa ta Sujada
(Fit 35.30—36.1)
1Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 2“Ga shi, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza. 3Na cika shi da Ruhuna, da hikima, da basira, da ilimi, da fasaha, 4don ya yi fasalin abubuwa na zinariya, da azurfa, da tagulla, 5da yankan duwatsu masu tamani na jerawa, da sassaƙa itace, da kowane irin aikin fasaha. 6Ga shi kuma, ni da kaina, na sa Oholiyab ɗan Ahisamak na kabilar Dan tare da shi, na kuma sa hikima a zukatan masu hikima, don su yi dukan abin da na umarce ka 7a kan alfarwar ta sujada da akwatin alkawari, da murfin da yake bisansa, da dukan kayayyakin da yake cikin alfarwar, 8da teburin da kayayyakinsa, da alkuki na zinariya tsantsa tare da dukan kayayyakinsa, da bagaden ƙona turare, 9da bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayayyakinsa, da daron da gammonsa, 10da saƙaƙƙun tufafi, wato da tsarkakakkun tufafin Haruna da na 'ya'yansa maza domin aikin firistoci, 11da man keɓewa, da turaren nan mai ƙanshi domin Wuri Mai Tsarki. Za su yi su duka kamar yadda na umarce ka.”
Ranar Hutawa
12Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 13“Faɗa wa Isra'ilawa, ‘Sai ku kiyaye Asabar domin shaida tsakanina da ku da zuriyarku har abada, domin ku sani ni ne Ubangiji wanda ya keɓe ku. 14Ku kiyaye ranar Asabar gama tsattsarkar rana ce a gare ku. Duk wanda ya tozarta ta, za a kashe shi, duk wanda ya yi aiki kuma a cikinta za a raba shi da jama'arsa. 15#Fit 20.8-11; 23.12; 34.21; 35.2; L.Fir 23.3; M.Sh 5.12-14 A kwana shida za a yi aiki, amma rana ta bakwai ranar hutawa ce tsattsarka ta saduda ga Ubangiji, don haka duk wanda ya yi kowane irin aiki a cikinta za a kashe shi. 16Domin wannan fa Isra'ilawa za su kiyaye ranar Asabar, su kiyaye ta dukan zamanansu, gama madawwamin alkawari ne. 17#Fit 20.11 Ranar za ta zama dawwamammiyar shaida tsakanina da Isra'ilawa, cewa a kwana shida ni Ubangiji na yi sama da ƙasa, amma a rana ta bakwai na ajiye aiki, na huta’ ”
18Sa'ad da ya gama magana da Musa a kan Dutsen Sina'i, sai ya ba shi alluna biyu na shaida, allunan duwatsu rubatattu da yatsan Allah.
Currently Selected:
Fit 31: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979