Fit 22
22
Dokokin Biya
1“Idan mutum ya saci sa ko tunkiya, ya yanka ko ya sayar, zai biya shanu biyar a maimakon sa, tumaki huɗu maimakon tunkiya. 2In aka iske ɓarawo yana cikin ƙoƙarin shiga ya yi sata, aka buge shi har ya mutu, to, ba za a nemi alhakin jininsa ga kowa ba, 3sai dai ko in gari ya riga ya waye. Dole ɓarawon ya yi cikakkiyar ramuwa, in kuwa ba shi da abin biya, a sayar da shi a biya abin da ya satar. 4In kuwa aka iske dabbar da ya satar a hannunsa da rai, ko sa, ko jaki, ko tunkiya, lalle ne ya biya riɓi biyu.
5“In mutum ya kai dabbarsa kiwo a saura ko a garka, ya bar ta, ta yi ɓarna a gonar wani, ko a gonar inabin wani, sai a sa mai dabbar ya biya tara daga amfanin gonarsa mafi kyau duka.
6“Idan wuta ta tashi a jeji ta ƙone tarin hatsi, ko hatsin da yake tsaye, ko gona, wanda ya sa wutar lalle ya biya cikakkiyar ramuwa.
7“Idan mutum ya ba amininsa amanar kuɗi, ko amanar kadara, amma aka sace, in aka sami ɓarawon, a sa shi ya biya ninki biyu. 8In kuwa ba a sami ɓarawon ba, sai a kawo maigidan a gaban Allah don a tabbatar babu hannunsa a cikin dukiyar amininsa.
9“A kowane laifi na cin amana, ko sa ne, ko jaki, ko tunkiya, ko tufa, ko kowane ɓataccen abu, da abin da aka samu a hannun wani, in akwai jayayya, za a kawo mutumin nan a gaban Allah. Wanda Allah ya ce shi ne da laifi, sai ya biya wa ɗayan ninki biyu.
10“In mutum ya bai wa amininsa amanar jaki, ko sa, ko tunkiya ko kowace irin dabba, amma dabbar ta mutu, ko ta yi rauni, ko ta ɓace, in ba shaida, 11rantsuwa ce za ta raba tsakaninsu don a tabbatar babu hannunsa a dukiyar amininsa, mai dukiyar kuwa ya yarda da rantsuwar. Wanda aka bai wa amanar ba zai biya ba. 12In dai sacewa aka yi, sai ya biya mai shi. 13Idan kuwa naman jeji ne ya kashe ta, zai nuna gawar don shida. Ba zai yi ramuwar abin da naman jeji ya kashe ba.
14“Idan mutum ya yi aron wani abu a wurin maƙwabcinsa, in abin ya yi rauni ko ya mutu, sa'ad da mai abin ba ya nan, lalle ne ya yi ramuwa. 15Amma in mai abin yana wurin, wanda ya yi aro ba zai yi ramuwa ba. Idan kuwa jingina ce aka yi, kuɗin jinginar ne ramuwar.”
Dokokin Addini da na Inganta Halin Kirki
16 #
M.Sh 22.28,29 “Idan mutum ya rarrashi budurwa wadda ba a tashinta, har ya ɓata ta, sai ya biya sadaki, ya aure ta. 17Amma idan mahaifinta bai yarda ya ba da ita gare shi ba, sai mutumin ya ba da sadaki daidai da abin da akan biya domin budurwa.
18 #
M.Sh 18.10,11 “Kada a bar mace mai sihiri ta rayu.
19 #
L.Fir 18.23; 20.15,16; M.Sh 27.21 “Duk wanda ya kwana da dabba, lalle kashe shi za a yi.
20 #
M.Sh 17.2-7
“Wanda ya miƙa hadaya ga wani allah, ba ga Ubangiji ba, sai a hallaka shi ɗungum.
21 #
Fit 23.9; L.Fir 19.33,34; M.Sh 24.17,18; 27.19 “Kada ku wulakanta baƙo ko ku zalunce shi, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar. 22Kada ku ci zalun marayu da gwauraye. 23In kun tsananta musu, ba shakka za su yi kuka gare ni, ni kuma, hakika zan ji kukansu. 24Zan husata, in sa a kashe ku cikin yaƙi, matanku, su ma, su zama gwauraye, 'ya'yanku kuwa su zama marayu.
25 #
L.Fir 25.35-38; M.Sh 15.7-11; 23.19,20 “Idan kun ranta wa jama'ata matalauta da suke tsakaninku kuɗi, ba za ku zama musu kamar masu ba da rance da ruwa ba. Kada ku nemi ruwan kuɗin daga gare su. 26#M.Sh 24.10-13 In har wani ya karɓi rigar amininsa jingina, lalle ne ya mayar masa da ita kafin faɗuwar rana. 27Gama wannan ne kaɗai mayafinsa, da shi zai rufe huntancinsa. Da me zai rufa ya yi barci? Zan amsa masa kuwa in ya yi kuka gare ni, gama cike nake da juyayi.
28 #
A.M 23.5
“Kada ku saɓi Allah, kada kuma ku zagi mai mulkin jama'arku.
29“Kada ku yi jinkirin fitar da zakar amfanin gonarku ta hatsi da ta abin matsewa.
“'Ya'yan farinku, maza, kuma za ku ba ni su. 30Haka kuma za ku yi da 'ya'yan farin shanunku, da na awakinku, da na tumakinku. Ɗan farin zai yi kwana bakwai tare da uwar, amma a rana ta takwas za ku ba ni shi.
31 #
L.Fir 17.15
“Za ku zama keɓaɓɓun mutane a gare ni. Kada ku ci dabbar da naman jeji ya yayyage shi, sai ku jefa wa karnuka.”
Currently Selected:
Fit 22: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979