Esta 7
7
Haman Ya Fāɗa a Ramin da Ya Haƙa
1Sarki da Haman kuwa suka tafi wurin Esta, gun liyafa. 2A rana ta biyu, sa'ad da suke shan ruwan inabi, sai sarki ya sāke ce wa Esta, “Mece ce bukatarki, sarauniya Esta? Za a yi miki. Mene ne roƙonki? Za a ba ki, ko da rabin mulkina ne.”
3Sai Esta ta ce, “Ya sarki, idan na sami tagomashi a wurinka, idan kuma sarki ya yarda, bukatata ita ce a bar ni da raina, roƙona kuma shi ne a bar mutanena. 4Gama an sayar da mu, ni da mutanena, don a hallaka mu, a karkashe, a ƙarasa mu. Da a ce an sayar da mu mu zama bayi, mata da maza, da na yi shiru, gama ba za a kwatanta wahalarmu da hasarar da sarki zai sha ba.”
5Sarki Ahasurus ya ce wa sarauniya Esta, “Wane ne shi, ina yake, wanda zai yi karambanin yin wannan?”
6Esta ta ce, “Haman ne, magabci, maƙiyi, mugu!”
Sai tsoro ya kama Haman a gaban sarki da sarauniya. 7Sarki kuwa ya tashi da fushi, ya tafi lambun fāda. Amma Haman ya tsaya don ya roƙi sarauniya Esta ta ceci ransa, gama ya ga sarki yana niyyar hukunta shi. 8Da sarki ya koma daga lambun fāda zuwa inda suke shan ruwan inabi, sai ga Haman ya fāɗi a kan shimfiɗar da Esta take zaune. Sai sarki ya ce, “Har ma zai ci mutuncin sarauniya a gabana, a gidana?”
Da dai sarki ya faɗi haka, sai bābāni suka cafe Haman. 9Sa'an nan Harbona, ɗaya daga cikin bābānin da yake yi wa sarki hidima ya ce, “Ga shi ma, Haman ya riga ya shirya gungumen itace a gidansa, mai tsayi kamu hamsin, inda zai rataye Mordekai wanda ya ceci sarki ta wurin maganarsa.”
Sai sarki ya ce, “A rataye Haman a gungumen.”
10Aka kuwa rataye Haman a gungumen itace da ya shirya zai rataye Mordekai. Sa'an nan sarki ya huce.
Currently Selected:
Esta 7: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979