YouVersion Logo
Search Icon

Esta 2

2
Esta Ta Zama Sarauniya
1Bayan waɗannan abubuwa, sa'ad da sarki Ahasurus ya huce daga fushinsa, sai ya tuna da abin da Bashti ta yi, da dokar da aka yi a kanta. 2Sa'an nan barorin sarki waɗanda suke yi masa hidima suka ce masa, “Bari a samo wa sarki 'yan mata, budurwai, kyawawa. 3Bari kuma sarki ya sa shugabanni a cikin dukan lardunan mulkinsa su tara dukan kyawawan 'yan mata, budurwai, a gidan matan kulle a masarauta a Shushan, ƙarƙashin Hegai bābā na sarki, wanda yake lura da mata. A riƙa ba budurwan man shafawa. 4Bari sarki ya zaɓi budurwar da ta gamshe shi, ta zama sarauniya maimakon Bashti.”
Sarki fa ya ji daɗin wannan shawara, ya kuwa yi haka ɗin.
5Akwai wani Bayahude a masarauta a Shushan, mai suna Mordekai ɗan Yayir, ɗan Shimai, ɗan Kish mutumin Biliyaminu. 6#2Sar 24.10-16; 2Tar 36.10 An kamo shi a Urushalima tare 'yan zaman talala waɗanda aka kwashe tare da Yekoniya Sarkin Yahuza, wanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kai su zaman talala. 7Mordekai ne ya goyi Hadassa, wato Esta, 'yar kawunsa, gama ita marainiya ce. Ita kuwa kyakkyawa ce. Sa'ad da iyayenta suka rasu, sai Mordekai ya karɓe ta tankar 'yarsa.
8Sa'ad da aka yi shelar dokar sarki, aka kuma tattara 'yan mata a masarauta a Shushan, a hannun Hegai, sai aka ɗauko Esta zuwa fādar sarki, aka sa ta a hannun Hegai wanda yake lura da mata. 9Esta kuwa ta gamshi Hegai, ta kuma sami farin jini a wurinsa, sai nan da nan ya ba ta man shafawa, da rabon abincinta, da zaɓaɓɓun kuyangi guda bakwai daga fādar sarki. Ya kuma kai ta da kuyanginta a wuri mafi kyau na gidan matan kulle.
10Esta ba ta riga ta bayyana asalin mutanenta, da danginta ba, gama Mordekai ya umarce ta kada ta yi. 11Kowace rana Mordekai yakan zo shirayin gidan matan kulle don ya san yadda Esta take.
12Sa'ad da lokacin kowace budurwa ya yi da za ta shiga wurin sarki Ahasurus, bayan da ta riga ta yi wata goma sha biyu na ka'idar yin kwalliyar mata, wato takan shafe jiki da man ƙanshi wata shida, ta kuma shafe jiki da turare da man shafawa wata shida, 13sa'an nan budurwar za ta shiga wurin sarki, sai a ba ta dukan abin da take bukata ta ɗauko daga gidan matan kullen zuwa fādar sarki. 14Takan tafi da yamma, ta koma gidan matan kulle na biyu da safe, a hannun Shawashgaz, bābā na sarki, wanda yake lura da ƙwaraƙwarai. Ba za ta ƙara zuwa wurin sarki ba, sai ko ta sami farin jini a wurin sarki sa'an nan a kirawo ta.
15Sa'ad da lokacin Esta 'yar Abihail, kawun Mordekai, wadda Mordekai ya karɓe ta tankar 'yarsa, ya yi da za ta shiga wurin sarki, ba ta bukaci kome ba, sai dai abin da Hegai, bābā na sarki, wanda yake lura da mata, ya ce. Esta kuwa tana da farin jini a idon duk wanda ya gan ta. 16Sa'ad da aka kai Esta wurin sarki Ahasurus a fādarsa a wata na goma, wato watan Tebet, a shekara ta bakwai ta sarautarsa, 17sai sarki ya ƙaunaci Esta fiye da dukan sauran matan. Ta kuwa sami alheri da farin jini a wurinsa fiye da sauran budurwan, saboda haka ya sa kambin sarauta a kanta. Ya naɗa ta sarauniya maimakon Bashti. 18Sarki kuwa ya yi wa sarakunansa da barorinsa ƙasaitaccen biki saboda Esta. Ya kuma ba larduna hutu, ya ba da kyautai da yawa irin na sarauta.
Mordekai Ya Ceci Ran Sarki
19Sa'ad da aka tara budurwai a karo na biyu, Mordekai yana zaune a ƙofar sarki. 20Har yanzu dai Esta ba ta bayyana asalin danginta da mutanenta ba, kamar yadda Mordekai ya umarce ta, gama Esta tana yi wa Mordekai biyayya kamar ta yi tun lokacin da yake renonta.
21A kwanakin nan sa'ad da Mordekai yake zaune a ƙofar sarki, sai babani biyu na sarki, wato Bigtana da Teresh waɗanda suke tsaron ƙofar, suka yi fushi, har suka nema su kashe sarki Ahasurus. 22Wannan maƙarƙashiya ta sanu ga Mordekai, shi kuwa ya faɗa wa sarauniya Esta. Esta kuma ta faɗa wa sarki da sunan Mordekai. 23Sa'ad da aka bincika al'amarin aka tarar haka yake. Sai aka rataye mutum biyu ɗin a kan gumagumai. Aka kuma rubuta labarin a littafin tarihi a gaban sarki.

Currently Selected:

Esta 2: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy