M.Sh 5
5
Dokoki Goma
(Fit 20.1-17)
1Musa ya kirawo Isra'ilawa duka, ya ce musu, “Ya ku Isra'ilawa, ku ji dokoki da farillai waɗanda nake muku shelarsu a yau! Sai ku koye su, ku aikata su sosai. 2Ubangiji Allahnmu ya yi alkawari da mu a Horeb. 3Ba da kakanninmu ne Ubangiji ya yi wannan alkawari ba, amma da mu ne, mu duka waɗanda suke da rai a yau. 4Ubangiji ya yi muku magana fuska da fuska bisa dutsen ta tsakiyar wuta. 5Ni ne na tsaya a tsakanin Ubangiji da ku a lokacin don in faɗa muku maganar Ubangiji, gama kun ji tsoro saboda wutar, ba ku kuma hau dutsen ba.
“Ubangiji ya ce, 6‘Ni ne Ubangiji Allahnka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar daga gidan bauta.
7“ ‘Kada ka kasance da waɗansu gumaka, sai ni.
8 #
L.Fir 26.1; M.Sh 4.15-18; 27.15 “ ‘Kada ka yi wa kanka gunki, ko wata siffar abin da yake a sama a bisa, ko siffar abin da yake a duniya a ƙasa, ko siffar abin da yake a cikin ruwa a ƙarƙashin ƙasa. 9#Fit 34.6,7; L.Ƙid 14.18; M.Sh 7.9,10 Kada ka yi musu sujada, ko ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, Allah mai kishi ne, nakan hukunta 'ya'ya, da jikoki saboda laifin iyaye waɗanda suka ƙi ni. 10Amma nakan nuna ƙauna ga dubbai waɗanda suke ƙaunata, suna kiyaye umarnaina.
11 #
L.Fir 19.12
“ ‘Kada ka rantse da sunan Ubangiji Allahnka a kan ƙarya, gama Ubangiji ba zai kuɓutar da wanda yake rantsewa da sunansa a kan ƙarya ba.
12 #
Fit 16.23-30; 31.12-14 “ ‘Ka kiyaye ranar Asabar, ka riƙe ta da tsarki yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka. 13#Fit 23.12; 31.15; 34.21; 35.2; L.Fir 23.3Kwana shida za ka yi aikinka duka. 14Amma rana ta bakwai ranar hutu ce ta Ubangiji Allahnka. A cikinta ba za ka yi kowane irin aiki ba, kai da ɗanka, da baranka, da baranyarka, da sanka, da jakinka, da kowace dabbar da kake da ita, da baƙon da yake zaune tare da kai, don barorinka mata da maza su ma su huta kamarka. 15Ka tuna fa, dā kai bawa ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji Allahnka ya fisshe ka da dantse mai iko, mai ƙarfi. Domin haka Ubangiji Allahnka ya umarce ka ka kiyaye ranar Asabar.
16 #
M.Sh 27.16; Mat 15.4; 19.19; Mar 7.10; 10.19; Luk 18.20; Afi 6.2;
Afi 6.3
“ ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka domin ka yi tsawon rai, ka sami zaman lafiya a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
17 #
Far 9.6; L.Fir 24.17; Mat 5.21; 19.18; Mar 10.19; Luk 18.20; Rom 13.9; Yak 2.11 “ ‘Kada ka yi kisankai.
18 #
L.Fir 20.10; Mat 5.27; 19.18; Mar 10.19; Luk 18.20; Rom 13.9; Yak 2.11 “ ‘Kada ka yi zina.
19 #
L.Fir 19.11; Mat 19.18; Mar 10.19; Luk 18.20; Rom 13.9 “ ‘Kada ka yi sata.
20 #
Fit 23.1; Mat 19.18; Mar 10.19; Luk 18.20 “ ‘Kada ka yi shaidar zur a kan maƙwabcinka.
21 #
Rom 7.7; 13.9 “ ‘Kada ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka, ko gonarsa, ko barorinsa mata ko maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abu da yake na maƙwabcinka.’
22 #
Ibr 12.18,19 “Ubangiji ya faɗa wa taron jama'arku waɗannan dokoki da murya mai ƙarfi ta tsakiyar wuta, da girgije, da duhu baƙi ƙirin. Ya rubuta su a bisa alluna biyu na dutse, ya ba ni, ba abin da ya ƙara.”
Mutane Suka Ji Tsoro
(Fit 20.18-21)
23“Sa'ad da kuka ji murya tana fitowa daga duhu, harshen wuta kuma tana ci a bisa dutse, sai shugabannin kabilanku da dattawanku suka zo wurina, 24suka ce, ‘Ga shi, Ubangiji Allahnmu ya bayyana mana ɗaukakarsa da girmansa, mun kuma ji muryarsa a tsakiyar wutar. Yau mun ga Allah ya yi magana da mutum, duk da haka ya rayu. 25Don me za mu mutu yanzu? Gama wannan babbar wuta za ta cinye mu. Idan muka ci gaba da jin muryar Ubangiji Allahnmu, za mu mutu. 26Akwai wani ɗan adam wanda ya taɓa jin muryar Allah, Allah Mai Rai yana magana ta tsakiyar wuta yadda muka ji, har ya rayu? 27Kai, ka matsa kusa, ka ji dukan abin da Ubangiji Allahnmu zai faɗa, sa'an nan ka mayar mana da dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya faɗa maka. Za mu ji, mu kuma aikata.’
28“Ubangiji kuwa ya ji maganarku wadda kuka yi mini, sai ya ce, ‘Na ji maganar da jama'an nan suka yi maka, abin da suka faɗa daidai ne. 29Da ma kullum suna da irin wannan zuciya ta tsorona, da za su kiyaye dukan umarnaina, zai zama fa'ida gare su da 'ya'yansu har abada. 30Tafi, ka faɗa musu su koma cikin alfarwansu. 31Amma kai ka tsaya nan a wurina don in faɗa maka dukan umarnai, da dokoki, da farillai, waɗanda za ka koya musu su kiyaye a ƙasar da nake ba su, su mallake ta.’
32“Sai ku lura ku yi daidai bisa ga abin da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, kada ku kauce dama ko hagu. 33Sai ku bi hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku don ku rayu, ku zauna lafiya, ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku mallaka.”
Currently Selected:
M.Sh 5: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979