YouVersion Logo
Search Icon

Dan 3

3
Ceto daga Tanderun Gagarumar Wuta
1Sarki Nebukadnezzar ya yi gunki na zinariya wanda tsayinsa kamu sittin ne, fāɗinsa kuma kamu shida. Ya kafa shi a filin Dura wanda yake a lardin Babila. 2Sa'an nan ya aika a kirawo su hakimai, da wakilai, da su muƙaddasai, da 'yan majalisa, da su ma'aji, da alƙalai, da masu mulki, da dukan ma'aikatan larduna, su zo, su halarci bikin keɓewar gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa. 3Sai hakimai, da wakilai, da su muƙaddasai, da 'yan majalisa, da su ma'aji, da alƙalai, da masu mulki, da dukan ma'aikatan larduna suka taru don keɓewar gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa. Suka kuma tsaya a gaban gunkin. 4Mai shela ya ta da murya da ƙarfi, ya ce, “An umarce ku, ya ku jama'a, da al'ummai, da harsuna mabambanta, 5cewa sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi, ku yi sujada ga gunkin zinariyan nan da sarki Nebukadnezzar ya kafa. 6Duk wanda bai fāɗi ƙasa ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a tanderun gagarumar wuta.” 7Don haka da dukan mutane, da al'ummai, da harsuna mabambanta sun ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai suka fāɗi ƙasa, suka yi sujada ga gunkin zinariya wanda sarki Nebukadnezzar ya kafa.
8A lokacin sai waɗansu Kaldiyawa suka tafi, suka yi ƙarar Yahudawa. 9Suka ce wa sarki Nebukadnezzar, “Ranka ya daɗe. 10Kai ne ka yi doka, cewa duk mutumin da ya ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ya fāɗi ƙasa, ya yi sujada ga gunkin zinariya. 11Duk wanda bai fāɗi ƙasa ya yi sujada ba, za a jefa shi a tanderun gagarumar wuta. 12Akwai waɗansu Yahudawa waɗanda ka naɗa su su lura da harkokin lardin Babila, wato Shadrak, da Meshak, da Abed-nego. Waɗannan mutane fa, ya sarki, ba su kula da kai ba, ba su bauta wa allolinka ba, ba su kuma yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa ba.”
13Nebukadnezzar fa, ya husata ya umarta a kawo Shadrak, da Meshak, da Abed-nego. Sai aka kawo su gaban sarki. 14Nebukadnezzar ya ce musu, “Ko gaskiya ne, wai kai Shadrak, da Meshak, da Abed-nego ba ku bauta wa allolina ba, ba ku kuma yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa ba? 15Yanzu, idan kuna so, sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi ƙasa, ku yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa. Idan kun yi haka, da kyau. Amma idan ba ku yi sujadar ba, nan take za a jefa ku a tanderun gagarumar wuta, in ga ko wane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”
16Shadrak, da Meshak, da Abed-nego kuwa suka amsa wa sarki suka ce, “Ya maigirma Nebukadnezzar, ba mu bukatar mu amsa maka da kome a kan wannan al'amari. 17Idan haka ne, Allahnmu wanda muke bauta wa, yana da iko ya cece mu daga tanderun gagarumar wuta, zai kuwa kuɓutar da mu daga hannunka, ya sarki. 18Ko ma bai cece mu ba, ka sani fa ya sarki, ba za mu bauta wa allolinka, ko kuma mu yi wa gunkin zinariya da ka kafa sujada ba.”
19Sai Nebukadnezzar ya husata ƙwarai da Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, har fuskarsa ta sāke. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar, har sau bakwai fiye da yadda take a dā. 20Sa'an nan ya umarci waɗansu ƙarfafan mutane daga cikin sojojinsa su ɗaure Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, su jefa su a tanderun gagarumar wuta. 21Sai aka ɗaure su suna saye da rigunansu da wandunansu, da hulunansu, da sauran tufafinsu, aka jefa su a tanderun gagarumar wuta. 22Tsananin umarnin sarki ya sa aka haɓaka wutar, sai harshen wutar ya kashe waɗanda suka jefa su Shadrak, da Meshak, da Abed-nego cikin wutar. 23Sa'an nan mutanen nan uku, wato Shadrak, da Meshak, da Abed-nego suka faɗi a tanderun gagarumar wuta a ɗaure.
24Sarki Nebukadnezzar kuwa ya zabura ya miƙe tsaye, cike da mamaki. Ya ce wa manyan fādawansa, “Ashe, ba mutum uku ne muka jefa a wuta ba?”
Su kuwa suka amsa wa sarki suka ce, “Ba shakka, haka yake, ranka ya daɗe.”
25Sarki ya ce, “Amma ina ganin mutum huɗu a sake, suna tafiya a tsakiyar wuta, ba kuma abin da ya same su, kamannin na huɗun kuwa kamar na ɗan alloli.”
An Saki Samari Uku na Yahudawa tare da Ƙarin Girma
26Nebukadnezzar fa ya matso kusa da ƙofar tanderun gagarumar wuta, ya ce, “Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, bayin Allah Maɗaukaki, ku fito, ku zo nan!” Sai Shadrak, da Meshak, da Abed-nego suka fita daga cikin wutar. 27Sa'an nan su hakimai, da wakilai, da muƙaddasai, da manyan 'yan majalisa suka taru, suka ga lalle wutar ba ta yi wa jikunan mutanen nan lahani ba, gashin kawunansu bai ƙuna ba, tufafinsu ba su ci wuta ba, ko warin wuta babu a jikinsu.
28Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, wanda ya aiko da mala'ikansa, ya ceci bayinsa masu dogara gare shi, waɗanda kuma ba su yarda su bi umarnin sarki ba, amma suka gwammace a ƙone su maimakon su bauta wa gunki, ko su yi masa sujada, sai dai ga Allahnsu kaɗai. 29Domin haka ina ba da wannan umarni cewa, ‘Dukan jama'a, ko al'umma, ko harshe wanda zai yi saɓon Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, za a yanyanka su gunduwa gunduwa, a ragargaje gidajensu, gama ba wani allah wanda zai yi wannan irin ceto.’ ”
30Sa'an nan sarki ya ƙara wa Shadrak, da Meshak, da Abed-nego girma a lardin Babila.

Currently Selected:

Dan 3: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in