Amos 6
6
Halakar Isra'ila
1Taku ta ƙare, ku da kuke zaman
sakewa a Sihiyona,
Da ku da kuke tsammani kuna
zaman lafiya a Samariya,
Ku da kuke manyan mutane
Na wannan babbar al'umma ta
Isra'ila,
Waɗanda jama'a suke zuwa a gare su
neman taimako!
2Ku je ku duba a birnin Kalne.
Sa'an nan ku zarce zuwa babban
birnin Hamat,
Har zuwa birnin Gat ta Filistiyawa.
Sun fi mulkin Yahuza da Isra'ila ne?
Ko kuwa, yankin ƙasarsu ya fi
naku?
3Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannan
rana ta masifa,
Amma ga shi, goyon bayan hargitsi
kuke ta yi,
Ta wurin ayyukanku.
4Taku ta ƙare, ku da kuke kwance
kan gadajen hauren giwa,
Kuna jin daɗin miƙe jiki a dogayen
kujerunku,
Ku ci naman maraƙi da na rago.
5Kukan so ku tsara waƙoƙi kamar
yadda Dawuda ya yi,
Ku raira su da garayu.
6Da manyan kwanoni kuke shan
ruwan inabi,
Ku shafe jiki da mai mafi kyau,
Amma ba ku yin makoki saboda
lalacewar Isra'ila.
7Don haka, ku ne na fari da za a sa su
yi ƙaura
Bukukuwanku da shagulgulanku za
su ƙare.
8Ubangiji kansa ne ya rantse.
Ubangiji Allah Mai Runduna ya ce,
“Ba na son girmankai na jama'ar
Isra'ila.
Ba na son fādodinsu.
Zan ba da birnin da dukan abin da
yake cikinsa ga abokan gābansu.”
9Ko da a ce mutum goma ne suka ragu a gida guda, duk za su mutu. 10Sa'ad da dangin mamacin ya shiga don ya fitar da gawar, ya ƙone, sai ya yi kira ga ko wane ne da yake ɓoye a gidan, ya ce, “Ko akwai wani kuma a nan?”
Sai a amsa, “A'a.”
Zai ce, “Kul! Kada a ambaci sunan Ubangiji.” 11Sa'ad da Ubangiji ya ba da umarni, babban gida da ƙarami rushewa za su yi.
12Dawakai sukan yi sukuwa a
duwatsu?
Ana huɗan teku da garmar
shanu?
Duk da haka kuka mai da adalci
dafi,
Kuka mai da nagarta, mugunta.
13Kuna fariyar cin garin Lodebar, wato
wofi, da yaƙi.
Kun ce, “Ƙarfinmu ya isa har mu ci
Karnayim, wato ƙaho biyu, da
yaƙi.”
14Ubangiji Allah Mai Runduna
kansa, ya amsa ya ce,
“Zan aiko da wata al'umma ta yi
gāba da ku, ya Isra'ilawa.
Za ta matse muku
Tun daga mashigin Hamat wajen
arewa,
Har zuwa Kwarin Urdun a kudu.”
Wahayi uku na Halaka
Currently Selected:
Amos 6: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979