A.M 27
27
Bulus Ya Shiga Jirgi zuwa Roma
1Da aka shirya mu tashin jirgin ruwa zuwa ƙasar Italiya, sai suka danƙa Bulus da waɗansu 'yan sarƙa a hannun wani jarumi, mai suna Yuliyas, na ƙungiyar Augustas. 2Da muka shiga wani jirgi na Adaramitiya, mai shirin tashi zuwa waɗansu garuruwan da suke gaɓar Asiya, muka fara tafiya. Aristarkus kuwa, wani mutumin Tasalonika ta ƙasar Makidoniya, na tare da mu. 3Kashegari ga mu a Sidon. Yuliyas kuwa ya yi wa Bulus alheri, ya ba shi izini ya je ya gano abokansa, su yi masa taimako. 4Da muka tashi daga nan a jirgin ruwa sai muka zaga ta bayan tsibirin Kubrus, saboda iska tana gāba da mu. 5Bayan da muka haye bahar ɗin da yake kusa da kasar Kilikiya da ta Bamfiliya, muka isa Mira ta ƙasar Likiya. 6A nan jarumin ya sami wani jirgin Iskandariya mai zuwa ƙasar Italiya, ya sa mu a ciki. 7Muka yi kwana da kwanaki muna tafiya kaɗan kaɗan, har da ƙyar muka kai kusa da Kinidas. Da dai iska ta hana mu ci gaba, muka zaga ta bayan tsibirin Karita kusa da Salmoni. 8Muna bin gefen gaɓarsa da ƙyar, har muka isa wani wuri mai suna Amintacciyar Mafaka, wadda take kusa da birnin Lasiya.
9Da yake an ɓata lokaci mai yawa, tafiyar ma ta riga ta zama mai hatsari, lokacin azumi kuwa ya wuce, sai Bulus ya gargaɗe su, 10ya ce musu, “Ya ku jama'a, na dai ga tafiyar nan za ta zamanto da masifa da hasara mai yawa, ba wai ta kaya da jirgi kawai ba, har ma ta rayukanmu.” 11Amma jarumin soja, ya fi mai da hankali ga maganar mai tuƙin jirgin da kuma ta mai jirgin, a kan abin da Bulus ya faɗa. 12Da yake mafakar nan ba ta kamaci jirage su ci damuna a ciki ba, sai yawanci suka kawo shawara a tashi daga nan, ko ta ƙaƙa su iya kaiwa Finikiya, wata mafakar tsibirin Karita, mai duban gabas maso arewa da kuma gabas maso kudu, su ci damuna a can.
Hadiri a Teku
13Da iska ta buso daga kudu sannu sannu, a tsammaninsu muradinsu ya biya ke nan, sai suka janye anka suka bi ta gefen tsibirin Karita gab da gaci. 14Ba da jimawa ba kuwa sai ga wata gawurtacciyar iska da ake kira Yurokilidon ta bugo daga tsibirin. 15Da iskar ta bugo jirgin, har ya kasa fuskantarta, sai muka sallama mata, ta yi ta kora mu. 16Da muka bi ta jikin wani ɗan tsibiri wai shi Kauda muka samu muka yi iko da ƙaramin jirginmu da ƙyar. 17Bayan suka jawo ƙaramin jirgi ɗin a cikin babban jirgi, sai suka yi dabara suka ɗaɗɗaura igiyoyi ta gindin babban jirgin, suka rage shi. Don kuma gudun kada a fyaɗa su a yashin nan na Sirtis mai haɗiye kome, suka sauke filafilai, aka kora jirgin haka. 18Saboda hadiri yana sa mu tangaɗi ƙwarai da gaske, kashegari sai suka fara watsar da kayan da jirgin ya ɗauko, a ruwa. 19A rana ta uku kuma, su da kansu suka jefar da kayan aikin jirgin. 20Da dai muka yi kwana da kwanaki ba mu ga rana ko taurari ba, gawurtacciyar iskar hadiri kuma ta yi ta bugunmu, sai muka fid da zuciya da tsira.
21Da yake an daɗe ba cin abinci, sai Bulus ya miƙe a tsaye a tsakiyarsu, ya ce, “Ya ku jama'a, da kun ji maganata, da ba ku taso daga tsibirin Karita kun fāɗa wannan masifa da hasara ba. 22To, a yanzu, ina yi muku gargaɗi ku yi ƙarfin hali, don ba wanda zai yi hasarar ransa a cikinku, sai dai a yi hasarar jirgin. 23Don a daren jiya wani mala'ikan Allah wanda ni nasa ne, nake kuma bauta masa, ya tsaya kusa da ni, 24ya ce, ‘Kada ka ji tsoro Bulus, lalle za ka tsaya a gaban Kaisar, ga shi kuma, Allah ya amsa ya yardar maka duk abokan tafiyarka su tsira.’ 25Saboda haka, sai ku yi ƙarfin hali, ya ku jama'a, domin na gaskata Allah a kan cewa, yadda aka faɗa mini ɗin nan, haka za a yi. 26Amma fa lalle ne a fyaɗa mu a wani tsibirin.”
27A dare na goma sha huɗu, ana ta kora mu sakaka a bahar Adariya, wajen tsakar dare sai masu tuƙi suka zaci mun yi kusa da ƙasa. 28Sai suka gwada zurfin ruwan, suka sami gaba ashirin, da muka ci gaba kaɗan, sai suka sāke gwadawa, suka sami gaba goma sha biyar. 29Don gudun kada a fyaɗa mu a kan duwatsu, sai suka saki anka guda huɗu na bayan jirgin, suka ƙagauta gari ya waye. 30Masu tuƙi suna neman gudu daga jirgin ke nan, har sun zura ƙaramin jirgi a cikin ruwa, wai don a ga kamar za su ja su anka ɗin ne daga goshin jirgin su sake su, 31sai Bulus ya ce da jarumin yaki da kuma sojan. “In mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba yadda za a yi ku tsira.” 32Sai sojan suka yayyanke igiyoyin ƙaramin jirgin, suka bar shi ya bi ruwa.
33Da gari ya yi kusan wayewa sai Bulus ya roƙe su su taɓa ɗan abinci, ya ce, “Yau fa kwana goma sha huɗu ke nan kuke zaman jira, ba wani abin da kuka ci. 34Saboda haka, ina roƙonku ku ci abinci, don lafiyarku, tun da yake ba wanda ko gashin kansa zai yi ciwo a cikinku.” 35Da ya faɗi haka, ya ɗauki curin gurasa, ya yi godiya ga Allah a gabansu duka, sa'an nan ya gutsuttsura ya fara ci. 36Sai duk suka farfado, su ma kansu suka ci abinci. 37Mu duka a cikin jirgin kuwa mutum metan da saba'in da shida ne. 38Da suka ci suka ƙoshi, sai suka riƙa rage wa jirgin nauyi, suka yi ta zub da alkama a cikin ruwa.
Ragargajewar Jirgi
39Da gari ya waye ba su shaida ƙasar ba, amma dai sun lura da wani lungu da gaci mai yashi, sai kuma suka yi shawara cewa in mai yiwuwa ne su kai jirgin kan yashin. 40Sai suka daddatse su anka duka, suka bar su a ruwa, suna kuma ɓalle maɗaurin abin juyar da jirgin a lokacin, sa'an nan kuma suka ta da filafilan goshin jirgin daidai iska, suka doshi gaci. 41Amma da muka isa wata mahaɗar ruwa, sai suka tura jirgin ya dunguri yashi, har goshinsa ya cije ya kasa motsi, ƙarshensa kuma ya fara ragargejewa saboda haukan raƙuman ruwa. 42Sai sojan suka yi niyya su kashe 'yan sarka, don kada wani ya yi ninƙaya ya tsira. 43Amma jarumin da ya so ya ceci Bulus, ya hana i da nufinsu, ya kuma yi umarni duk waɗanda suka iya ruwa su fara fāɗawa zuwa gaci, 44sauran kuwa waɗansu suka hau katako, waɗansu kuma suka hau tarkacen jirgin. Da haka duk suka kai gaci lafiya.
Currently Selected:
A.M 27: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979