A.M 23
23
1Sai Bulus ya zuba wa majalisar ido ya ce, “Ya ku 'yan'uwa, bautar Allah nake yi da lamiri mai kyau har ya zuwa yau.” 2Sai Hananiya babban firist ya umarci waɗanda suke tsaye kusa da Bulus su buge bakinsa. 3#Mat 23.27,28 Sai Bulus ya ce masa, “Kai munafiƙi, kai ma Allah zai buge ka! Ashe, wato kana zaune kana hukunta ni bisa ga Shari'a ne, ga shi kuwa kana yin umarni a doke ni, a saɓanin Shari'a?” 4Sai waɗanda suke tsaye a wurin suka ce masa, “Babban firist na Allah za ka zaga?” 5#Fit 22.28 Sai Bulus ya ce, “Ai, ban sani shi ne babban firist ba, 'yan'uwa, don a rubuce yake cewa, ‘Kada ka munana shugaban jama'a.’ ”
6 #
A.M 26.5; Fili 3.5 Amma da Bulus ya ga sashe ɗaya Sadukiyawa ne, ɗayan kuma Farisiyawa, ya ɗaga murya a majalisar ya ce, “Ya 'yan'uwa, ni ma Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ga shi kuwa, saboda na sa zuciya ga tashin matattu ne ake yi mini shari'a.” 7Da ya faɗi haka sai gardama ta tashi a tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, har taron ya rabu biyu. 8#Mat 22.23; Mar 12.18; Luk 20.27 Sadukiyawa sun ce, wai ba tashin matattu, ba kuma mala'iku, ko ruhu. Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai. 9Sai ƙasaitacciyar hargowa ta tashi, waɗansu malamai kuma na ɗariƙar Farisiyawa suka miƙe a tsaye, suka yi ta yin matsananciyar jayayya, suna cewa, “Mu ba mu ga laifin mutumin nan ba. In wani ruhu ne ko mala'ika ya yi masa magana fa?” 10Da gardamar ta yi tsanani, don gudun kada su yi kaca-kaca da Bulus, shugaban ya umarci sojan su sauka su ƙwato shi daga wurinsu ƙarfi da yaji, su kawo shi a kagarar soja.
11Da daddare sai Ubangiji ya tsaya a kusa da Bulus, ya ce, “Ka yi ƙarfin hali, don kamar yadda ka shaide ni a Urushalima, haka kuma lalle ne ka shaide ni a Roma.”
Ƙulla Shawara a Kashe Bulus
12Da gari ya waye, Yahudawa suka gama baki suka yi rantsuwa, cewa ba za su ci ba, ba za su sha ba, sai sun kashe Bulus. 13Waɗanda suka ƙulla wannan makirci kuwa sun fi mutum arba'in. 14Sai suka je wurin manyan firistoci da shugabanni, suka ce, “Mun yi wata babbar rantsuwa, cewa za mu zauna ba ci ba sha sai mun kashe Bulus. 15Saboda haka, yanzu ku da majalisa ku shaida wa shugaban soja ya kawo muku shi, kamar kuna so ne ku ƙara bincika maganarsa sosai, mu kuwa a shirye muke mu kashe shi kafin ya iso.”
16To, ɗan 'yar'uwar Bulus ya ji labarin farkon da za su yi, ya kuma je ya shiga kagarar soja ya gaya wa Bulus. 17Bulus kuwa ya kira wani jarumi ya ce, “Ka kai saurayin nan wurin shugaba, yana da wata magana da zai faɗa masa.” 18Sai jarumin ya ɗauki saurayin ya kai shi gun shugaba, ya ce, “Ɗan sarƙan nan, Bulus, ya kira ni, ya roƙe ni in kawo saurayin nan a wurinka, don yana da wata maganar da zai gaya maka.” 19Sai shugaban ya kama hannun saurayin, ya ja shi a waje ɗaya, ya tambaye shi a keɓance, “Wace magana za ka gaya mini?” 20Yaron ya ce, “Yahudawa sun ƙulla za su roƙe ka ka kai musu Bulus majalisa gobe, kamar suna so su ƙara bincika maganarsa sosai. 21Amma kada ka yardar musu, don fiye da mutum arba'in daga cikinsu suna fakonsa, sun kuma yi rantsuwa a kan ba za su ci ba, ba za su sha ba, sai sun kashe shi. Yanzu kuwa a shirye suke, yardarka kawai suka jira.” 22Sai shugaban ya sallami saurayin ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa cewa ka sanar da ni maganar nan.”
An Aika da Bulus zuwa ga Mai Mulki Filikus
23Sa'an nan ya kira jarumi biyu ya ce, “Ku shirya soja metan, da barade saba'in, da 'yan māsu metan, su tafi Kaisariya da ƙarfe tara na daren nan.” 24Ya kuma yi umarni su shirya wa Bulus dabbobin da zai hau, don su kai shi wurin mai mulki Filikus lafiya. 25Ya kuma rubuta wasiƙa kamar haka:
26“Daga Kalaudiyas Lisiyas zuwa ga mafifici mai mulki Filikus. Gaisuwa mai yawa. 27Bayan haka mutumin nan, Yahudawa sun kama shi, suna kuma gab da kashe shi, sai na yi farat na je da soja na ƙwato shi, saboda na ji cewa shi Barome ne. 28Da ina so jin laifin da suke zarginsa a kai, sai na kai shi majalisarsu. 29Na kuwa tarar suna zarginsa a kan maganar Shari'arsu, amma laifin da suka ɗora masa bai kai ga kisa ko ɗauri ba. 30Da aka buɗa mini cewa akwai wani makircin da aka ƙulla masa, nan da nan na aika da shi a gare ka, na kuma umarci masu ƙararsa su faɗi ƙararsu a gabanka. Wassalam.”
31Saboda haka, sojan suka ɗauki Bulus, kamar yadda aka umarce su, suka kai shi Antibatiris da daddare. 32Kashegari kuma suka bar barade su ci gaba da shi, su kuwa suka koma kagarar soja. 33Da baraden suka isa Kaisariya, suka ba mai mulkin wasiƙar, suka kai Bulus a gabansa. 34Da ya karanta wasiƙar, ya tambayi Bulus ko shi mutumin wane lardi ne? Da ya ji daga Kilikiya yake, 35ya ce, “Zan saurari maganarka duka, in masu ƙararka sun zo.” Sai kuma ya yi umarni a tsare shi a fadar Hirudus.
Currently Selected:
A.M 23: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979