A.M 18
18
Bulus a Koranti
1Bayan haka Bulus ya tashi daga Atina ya tafi Koranti. 2Can ya tarar da wani Bayahude mai suna Akila, asalinsa kuwa mutumin Fantas ne, bai daɗe da zuwa daga ƙasar Italiya ba, tare da mata tasa Bilkisu, don wai Kalaudiyas ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya je wurinsu. 3Da yake kuma sana'arsu ɗaya ce, maɗinkan tanti ne, ya sauka a wurinsu, suka yi ta aiki tare. 4Ya kuma yi ta yin muhawwara a majami'a a kowace Asabar, yana ta rinjayar Yahudawa da al'ummai.
5Sa'ad da Sila da Timoti suka zo daga Makidoniya, Bulus ya dukufa a kan yin wa'azi, yana tabbatar wa Yahudawa, cewa Almasihu dai Yesu ne. 6Da suka mūsa masa, suna ta zaginsa, ya karkaɗe tufafinsa ya ce musu, “Alhakinku yana a wuyanku! Ni kam na fita. Daga yau wurin al'ummai zan je.” 7Sai ya tashi daga nan ya je gidan wani mutum mai suna Titus Yustus mai ibada, gidansa kuwa gab da majami'a yake. 8Sai Kirisbus, shugaban majami'ar ya ba da gaskiya ga Ubangiji, shi da jama'ar gidansa duka. Korantiyawa kuma da yawa da suka ji maganar Bulus suka ba da gaskiya, aka kuwa yi musu baftisma. 9Wata rana da daddare, Ubangiji ya yi wa Bulus wahayi, ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, sai dai ka yi ta wa'azi, kada ka yi shiru, 10domin ina tare da kai, ba kuma wanda zai fāɗa ka ya cuce ka, domin ina da mutane da yawa a wannan birni.” 11Sai Bulus ya zauna a nan har shekara ɗaya da wata shida, yana ta koyar da Maganar Allah a cikinsu.
12Amma sa'ad da Galiyo yake muƙaddashin ƙasar Akaya, Yahudawa suka tasar wa Bulus da nufi ɗaya suka kawo shi a gaban shari'a, 13suka ce, “Mutumin nan na rarrashin mutane, wai su bauta wa Allah ta hanyar da Shari'ar ta hana.” 14Bulus na shirin yin magana ke nan sai Galiyo ya ce wa Yahudawan, “Ku Yahudawa! Da ma wani laifi ya yi, ko munafunci, da sai in iya sauraronku. 15Amma tun da yake gardama ce kawai a kan kalmomi, da sunaye, da kuma shari'arku, ai, sai ku ji da ita, ku da kanku. Ni kam, ba ni da niyyar yin shari'a irin waɗannan abubuwa.” 16Sai ya kore su daga ɗakin shari'a. 17Sai duk suka kama Sastanisu, shugaban majami'a, suka yi masa dūka a gaban gadon shari'a. Amma Galiyo ko yă kula.
Bulus Ya Koma Antakiya ta Suriya
18 #
L.Ƙid 6.18
Bulus kuwa da ya ƙara kwanaki da yawa, bayan ya sausaye kansa a Kankiriya don ya cika wa'adin da ya ɗauka, ya yi bankwana da 'yan'uwa, ya shiga jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, tare da Bilikisu da Akila. 19Sai suka isa Afisa, a can ne kuma ya bar su, shi kuwa ya shiga majami'a ya yi muhawwara da Yahudawa. 20Sai suka roƙe shi ya ƙara jimawa a wurinsu, amma bai yarda ba. 21Sai dai ya yi bankwana da su, ya ce, “Zan dawo wurinku in Allah ya so.” Sa'an nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa.
22Da ya sauka a Kaisariya, sai ya je Urushalima, ya gaisa da Ikkilisiya, sa'an nan ya tafi Antakiya.
23Bayan da ya ɗan jima a nan, ya tashi ya zazzaga ƙasar Galatiya da ta Firijiya, yana bin gari gari, yana ƙarfafa dukan masu bi.
Afolos ya Yi Wa'azi a Afisa
24To, wani Bayahude mai suna Afolos ya zo Afisa. Shi kuwa asalinsa mutumin Iskandariya ne, masani ne kuwa, ya san Littattafai ƙwarai da gaske. 25An karantar da shi tafarkin Ubangiji, da yake kuma muhimmanci ne ƙwarai, yakan yi ta magana kan al'amuran Yesu, yana kuma koyar da su sosai, amma fa baftismar Yahaya kaɗai ya sani. 26Sai ya fara wa'azi gabagaɗi a majami'a, amma da Bilkisu da Akila suka ji maganarsa, suka ja shi a jika, suka ƙara bayyana masa tafarkin Allah sosai da sosai. 27Da ya so hayewa zuwa ƙasar Akaya, 'yan'uwa suka taimake shi, suka rubuta wa masu bi wasiƙa su karɓe shi hannu biyu biyu. Da kuwa ya isa, ya yi matuƙar taimako ga waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin alherin Ubangiji, 28don yā kayar da Yahudawa ƙwarai a gaban jama'a, yana tabbatar musu ta wurin Littattafai cewa Almasihu dai Yesu ne.
Currently Selected:
A.M 18: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979