YouVersion Logo
Search Icon

A.M 14

14
Bulus da Barnaba a Ikoniya
1To, a Ikoniya suka shiga majami'ar Yahudawa tare, suka yi wa'azi, har mutane masu yawa, Yahudawa da al'ummai, suka ba da gaskiya. 2Amma Yahudawa da suka ƙi bi, suka zuga al'ummai, suka ɓata tsakaninsu da 'yan'uwa. 3Sai Bulus da Barnaba suka daɗe a nan ƙwarai, suna wa'azi gabagaɗi bisa ga ikon Ubangiji, shi da ya shaida maganar alherinsa ta yarjin mu'ujizai da abubuwan al'ajabi ta hannunsu. 4Amma mutanen birni suka rarrabu, waɗansu suka koma bayan Yahudawa, waɗansu kuma bayan manzannin. 5Sa'ad da al'ummai da Yahudawa tare da shugabanninsu suka tasar wa manzannin, su wulakanta su, su jejjefe su da duwatsu, 6suka sami labari, suka gudu zuwa biranen Likoniya wato Listira da Darba, da kuma kewayensu. 7Nan suka yi ta yin bisharar.
An Jejjefi Bulus a Listira
8To, a Listira akwai wani mutum a zaune, wanda ƙafafunsa ba su da ƙarfi, gurgu ne tun da aka haife shi, bai ma taɓa tafiya ba. 9Yana sauraron wa'azin Bulus, sai Bulus ya zuba masa ido, da ya ga bangaskiyarsa ta isa a warkar da shi, 10ya ɗaga murya ya ce, “Tashi, ka tsaya cir.” Sai wuf ya zabura, har ya yi tafiya. 11Da taron suka ga abin da Bulus ya yi, suka ɗaga murya gaba ɗaya suna cewa da Likoniyanci, “Lalle, alloli sun sauko mana da siffar mutane!” 12Sai suka ce Barnaba shi ne Zafsa, Bulus kuwa don shi ne shugaban magana, wai shi ne Hamisa. 13Sai sarkin tsafin Zafsa, wanda ɗakin gunkinsa yake ƙofar gari, ya kawo bajimai da tutocin furanni ƙofar gari, yana son yin hadaya tare da jama'a. 14Amma da manzannin nan, Barnaba da Bulus, suka ji haka, suka kyakketa tufafinsu, suka ruga cikin taron, suna ɗaga murya suna cewa, 15#Fit 20.11; Zab 146.6 “Don me kuke haka? Ai, mu ma 'yan adam ne kamarku, mun dai kawo muku bishara ne, domin ku juya wa abubuwan banzan nan baya, ku juyo ga Allah Rayayye, wanda ya halicci sama, da ƙasa, teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu. 16Shi ne a zamanin dā, ya bar dukan al'ummai su yi yadda suka ga dama. 17Duk da haka kuwa bai taɓa barin kansa, ba shaida ba, domin yana yin alheri, shi da yake yi muku ruwan sama, da damuna mai albarka, yana ƙosar da ku da abinci, yana kuma faranta muku rai.” 18Duk da waɗannan maganganu da ƙyar suka hana jama'ar nan yin hadaya saboda su.
19Amma waɗansu Yahudawa suka zo daga Antakiya da Ikoniya, da suka rarrashi taron, suka jejjefe Bulus suka ja shi bayan gari, suna zato ya mutu. 20Amma da masu bi suka taru a kansa, sai ya tashi ya koma garin. Kashegari kuma ya tafi Darba tare da Barnaba. 21Bayan sun yi bishara a wannan gari, sun kuma sami masu bi da yawa, suka koma Listira da Ikoniya, da kuma Antakiya, 22suna ƙarfafa masu bi, suna yi musu gargaɗi su tsaya ga bangaskiya, suna cewa, sai da shan wuya mai yawa za mu shiga Mulkin Allah. 23Bayan kuma sun zaɓar musu dattawa a kowace Ikkilisiya, game da addu'a da azumi, suka danƙa su ga Ubangiji, wanda dā ma suka gaskata da shi.
Komawa Antakiya ta Suriya
24Da suka zazzaga ƙasar Bisidiya, suka isa ƙasar Bamfiliya. 25Da kuma suka faɗi Maganar a Bariyata, suka tafi Ataliya. 26Daga nan kuma suka shiga jirgin ruwa sai Antakiya, inda tun dā aka yi musu addu'a alherin Allah ya kiyaye su cikin aikin nan da yanzu suka gama. 27Da suka iso, suka tara jama'ar Ikkilisiya suka ba da labarin dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu, da kuma yadda ya buɗe wa al'ummai ƙofar bangaskiya. 28Sun kuwa jima a can tare da masu bi.

Currently Selected:

A.M 14: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in