YouVersion Logo
Search Icon

2Tas 3

3
Addu'a Dominmu
1Daga ƙarshe kuma 'yan'uwa, ku yi mana addu'a, Maganar Ubangiji ta yi saurin yaɗuwa, ta sami ɗaukaka, kamar yadda ta samu a gare ku, 2a kuma cece mu daga fanɗararrun mutane, mugaye. Don ba duka ne suke da bangaskiya ba. 3Amma Ubangiji mai alkawari ne, zai kuwa kafa ku, ya tsare ku daga Mugun nan. 4Mun kuma amince da ku a game da Ubangiji, cewa kuna bin umarnin da muka yi muku, za ku kuma riƙa bi. 5Ubangiji yă tattaro hankalinku a kan ƙaunar nan ta Allah, da kuma jimirin nan na Almasihu.
Wajibi Ne a Yi Aiki
6To, 'yan'uwa, muna yi muku umarni da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, ku fita daga sha'anin kowane ɗan'uwa malalaci, wanda ba ya bin ka'idodin da kuka samu a wurinmu. 7Ai, ku kanku kun san yadda ya kamata ku yi koyi da mu, domin sa'ad da muke a tare, ba mu nuna muku lalaci ba, 8ba mu kuwa ci abincin kowa a banza ba, sai dai mun sha wahala da fama, muna aiki dare da rana, don kada mu nawaita wa kowane ɗayanku. 9Ba don ba mu da halaliya a wurinku ba ne, a'a, sai dai don mu zama abin misali a gare ku kawai, don ku yi koyi da mu. 10Ai, ko dā ma, sa'ad da muke a tare, mun yi muku wannan umarni, cewa duk wanda ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci. 11Gama mun ji labari cewa waɗansunku malalata ne kawai, ba sa aikin kome, masu shisshigi ne kurum. 12To, irin waɗannan mutane muna yi musu umarni, muna kuma gargaɗinsu da izinin Ubangiji Yesu Almasihu, su riƙa aiki da natsuwa, suna ci da kansu. 13Amma ku 'yan'uwa, kada ku gaji da yin aiki nagari.
14In wani ya ƙi bin abin da muka faɗa a wasiƙar nan, sai fa ku lura da shi, kada ma ku yi cuɗanya da shi, don yă kunyata. 15Amma kada ku ɗauke shi a kan abokin gāba, sai dai ku gargaɗe shi a kan shi ɗan'uwa ne.
Sa Albarka
16To, Ubangiji kansa, mai zartar da salama, yă ba ku salama a koyaushe a kowane hali. Ubangiji ya kasance tare da ku duka.
17Ni Bulus, ni nake rubuto wannan Gaisuwa da hannuna. Ita ce kuwa shaidar kowace wasiƙata. Rubutun hannuna ke nan. 18Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku duka.

Currently Selected:

2Tas 3: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy