2Sam 3
3
1Gidan Saul da gidan Dawuda suka daɗe suna yaƙi da juna. Ƙarfin gidan Dawuda ya yi ta ƙaruwa, amma na gidan Saul ya yi ta raguwa.
'Ya'ya Maza da aka Haifa wa Dawuda a Hebron
(1Tar 3.1-4)
2'Ya'ya maza da aka haifa wa Dawuda a Hebron ke nan, Ahinowam Bayezreyeliya ta haifa masa ɗan farinsa, Amnon. 3Abigail, matar marigayi, Nabal Bakarmele, ta haifa masa ɗansa na biyu, Kileyab. Ma'aka 'yar Talmai, Sarkin Geshur, ta haifa masa ɗansa na uku, Absalom. 4Haggit ta haifa masa ɗansa na huɗu, Adonaija. Abital ta haifa masa ɗansa na biyar, Shefatiya. 5Matarsa Egla ta haifa masa ɗansa na shida, Itireyam. Dukan waɗannan a Hebron ne aka haife su.
Abner ya Bi Dawuda
6Abner ya ƙasaita sosai a gidan Saul a lokacin da ake yaƙi tsakanin jarumawan Saul da na Dawuda.
7Saul yana da ƙwarƙwara mai suna Rizfa, 'yar Aiya. Sai Ish-boshet ya ce wa Abner, “Me ya sa ka kwana da ƙwarƙwarar tsohona?”
8Abner ya husata saboda wannan magana, ya ce, “Kana zato ni maci amanar ƙasa ne? Kana tsammani ina wa ƙasar Yahuza aiki ne? Tun da farko ina ta nuna alheri ga gidan Saul, tsohonka, da 'yan'uwansa, da abokansa, ban kuwa ba da ka a hannun Dawuda ba. Amma ga shi, yau ka zarge ni da laifin kwartanci game da wannan mata. 9#1Sam 15.28 Allah ya la'anta ni, idan ban yi wa Dawuda abin da Ubangiji ya rantse masa ba, 10wato in mayar wa Dawuda da sarautar gidan Saul. In kafa kursiyin Dawuda a kan Isra'ila da kan Yahuza tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba.” 11Ish-boshet kuwa bai ce wa Abner uffan ba, don yana jin tsoronsa.
12Sai Abner ya aiki manzanni zuwa wurin Dawuda a Hebron, ya ce, “Ƙasar ta wane ne? Ka yi mini alkawari, ni kuwa zan goyi bayanka, in sa dukkan Isra'ilawa su bi ka.”
13Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi maka alkawari a kan wannan sharaɗi, ba za ka ga fuskata ba sai ka kawo mini matata, Mikal, 'yar Saul, sa'ad da za ka zo wurina.” 14#1Sam 18.27 Sa'an nan Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-boshet, ɗan Saul, ya ce, “Ka ba ni matata, Mikal, wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari ta Filistiyawa.” 15Sai Ish-boshet ya aika aka ƙwato Mikal daga wurin mijinta, Falti, ɗan Layish. 16Mijinta ya bi ta yana ta kuka har zuwa Bahurim. Sai Abner ya ce masa ya koma, ya kuwa koma.
17Abner ya shawarci dattawan Isra'ila, ya ce, “Dā ma can kuna so Dawuda ya sarauce ku. 18To, yanzu sai ku yarda ya sarauce ku, gama Ubangiji ya yi wa Dawuda alkawari ya ce, ‘Ta hannun bawana, Dawuda, zan ceci jama'ar Isra'ila daga hannun Filistiyawa, da na dukan abokan gābansu.’ ” 19Abner kuma ya yi magana da mutanen Biliyaminu, sa'an nan ya tafi ya faɗa wa Dawuda a Hebron abin da dukan Isra'ilawa da dukan kabilar Biliyaminu suka ga ya yi kyau, su yi.
20Abner tare da mutum ashirin suka zo wurin Dawuda a Hebron, Dawuda kuwa ya yi musu liyafa. 21Sai Abner ya ce wa Dawuda, “Zan tashi in tafi in tattara wa ubangijina sarki dukan Isra'ilawa, domin su yi alkawari da kai, kai kuma ka sarauce su yadda kake so.” Dawuda kuwa ya sallami Abner, ya tafi lafiya.
An Kashe Abner
22Sai ga barorin Dawuda da Yowab sun komo daga hari. Sun kawo ganima mai yawa. Abner kuwa ya riga ya tafi, gama Dawuda ya riga ya sallame shi, ya tafi lafiya. 23Da Yowab da sojojin da suke tare da shi suka iso, sai aka faɗa masa cewa, “Abner ɗan Ner ya zo wurin sarki, sarki kuwa ya bar shi ya tafi lafiya.”
24Sai Yowab ya tafi wurin sarki ya ce, “Me ke nan ka yi? Abner ya zo wurinka, me ya sa ka bar shi ya tafi lafiya? 25Ka sani Abner ɗan Ner ya zo ya ruɗe ka ne, ya san fitarka da shigarka, ya kuma san dukan abin da kake yi.”
26Da Yowab ya fita daga wurin Dawuda, sai ya aiki manzanni su bi bayan Abner. Suka komo da shi a rijiyar Sira, amma Dawuda bai sani ba. 27Sa'ad da Abner ya komo Hebron, sai Yowab ya raɓa da shi wajen ƙofar garin kamar zai gana da shi, sai ya soke shi a ruwan ciki, ya fāɗi ya mutu, saboda alhakin jinin ɗan'uwansa, Asahel. 28Daga baya sa'ad da Dawuda ya ji, sai ya ce, “Ni da mulkina baratattu ne a gaban Ubangiji daga alhakin jinin Abner ɗan Ner har abada. 29Allah ya sa alhakin jinin ya faɗa kan Yowab da dukan gidan ubansa. Ya sa kada a rasa mai ɗiga, ko kuturu, ko wanda yake dogara sanda, ko wanda aka kashe da takobi, ko wanda ba shi da abinci, a gidan Yowab.” 30Ta haka Yowab da ɗan'uwansa Abishai suka kashe Abner saboda ya kashe ƙanensu, Asahel, a wurin yaƙi a Gibeyon.
31Dawuda kuwa ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku kyakketa tufafinku, ku sa tsummoki, ku yi makoki domin Abner.” Sarki Dawuda kuwa ya bi bayan makara. 32Suka binne Abner a Hebron. Sarki ya ta da murya ya yi kuka a kabarin Abner. Dukan mutane kuma suka yi kuka. 33Sarki ya yi wannan makoki domin Abner, ya ce,
“Don me Abner zai mutu kamar wawa?
34Hannuwansa ba a ɗaure suke ba,
Ƙafafunsa kuma ba a dabaibaye suke ba.
Ya mutu kamar wanda mugayen mutane suka kashe.”
Dukan mutane suka yi kuka kuma saboda shi.
35Mutane kuwa suka zo su ba Dawuda magana, ko ya ci abinci tun rana ba ta faɗi ba. Amma Dawuda ya rantse ya ce, “Allah ya buge ni in mutu nan, idan na ɗanɗana abinci ko wani abu kafin rana ta faɗi.” 36Da mutanen suka lura, sai suka yarda da abin da sarki ya yi, suka kuma ji daɗin kowane abu da sarki ya yi. 37A wannan rana dukan mutanen Dawuda da dukan mutanen Isra'ila suka gane, ashe, ba nufin Dawuda ba ne a kashe Abner ɗan Ner. 38Sarki ya ce wa fādawansa, “Ba ku sani ba, basarake ne, babban mutum ne kuma ya faɗi a cikin Isra'ila yau? 39Yau na raunana, ko da yake ni sarki ne naɗaɗɗe. Waɗannan mutane, 'ya'yan Zeruya, sun fi ƙarfina, Ubangiji ya sāka wa mai aikata mugunta da muguntar da ya aikata.”
Currently Selected:
2Sam 3: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979