YouVersion Logo
Search Icon

2Sam 20

20
Tawayen Sheba
1 # 1Sar 12.16; 2Tar 10.16 Da can akwai wani mutumin banza, ana ce da shi Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Biliyaminu. Shi kuwa ya busa ƙaho, ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu kuwa da gado wurin ɗan Yesse. Ya Isra'ilawa, kowa ya gudu zuwa alfarwarsa.” 2Sai dukan Isra'ilawa suka janye jiki daga wurin Dawuda, suka bi Sheba, ɗan Bikri, amma mutanen Yahuza suka manne wa sarki tun daga Urdun har zuwa Urushalima.
3 # 2Sam 16.22 Da Dawuda ya koma gidansa a Urushalima, kwarakwaran nan nasa guda goma waɗanda ya bar su tsaron gida ya keɓe su a wani gida inda za a yi tsaronsu. Ya yi ta lura da su, amma bai shiga wurinsu ba. Haka suka zauna a keɓe, suna zaune kamar gwauraye.
4Sa'an nan sarki ya ce wa Amasa, “Ka tattaro mini mutanen Yahuza kafin kwana uku, kai kuma ka zo tare da su.” 5Sai Amasa ya tafi ya kira mutanen Yahuza, amma ya makara, bai zo a lokacin da aka ƙayyade masa ba. 6Dawuda kuma ya ce wa Abishai, “Sheba ɗan Bikri fa, zai ba mu wuya fiye da Absalom, sai ka ɗauki mutanena, ka bi sawunsa, don kada ya ci garuruwa masu garu har ya tsere mana.” 7Sa'an nan mutanen Yowab, wato Keretiyawa da Feletiyawa, da dukan jarumawa, suka bi bayan Abishai. Suka fita daga Urushalima don su bi sawun Sheba, ɗan Bikri.
8Sa'ad da suke a babban dutsen Gibeyon, Amasa ya zo ya tarye su. A lokacin nan Yowab yana saye da rigar yaƙi, ya sha ɗamara, yana kuma rataye da takobi a ɗamararsa. Da ya gabato, sai takobin ya faɗi. 9Yowab ya ce wa Amasa, “Abokina kana lafiya?” Yowab kuma ya kama gemun Amasa da hannun dama don ya sumbace shi. 10Amma Amasa bai lura Yowab yana da takobi a hannunsa ba. Yowab kuwa ya kirɓa masa takobin a ciki sau ɗaya, sai hanjin Amasa ya zuba ƙasa, ya mutu.
Sa'an nan Yowab da Abishai ɗan'uwansa suka bi sawun Sheba, ɗan Bikri. 11Sai ɗaya daga cikin samarin Yowab ya tsaya kusa da gawar Amasa ya ce, “Duk wanda yake son Yowab da duk wanda yake goyon bayan Dawuda, ya bi Yowab.” 12Gawar Amasa kuwa ta birkiɗe da jini tana a tsakiyar hanya. Da mutumin ya ga yadda dukan mutane suka tsaya, sai ya kawar da ita daga tsakiyar hanya zuwa cikin saura, ya rufe ta da tufa, gama dukan wanda ya ga gawar, sai ya ja, ya tsaya. 13Sa'ad da aka kawar da ita daga kan hanya, dukan mutane kuwa suka bi Yowab domin su bi sawun Sheba ɗan Bikri.
14Sai Sheba ya bibiya kabilan Isra'ila, har ya kai Abel-bet-ma'aka. Dukan dangin Beri kuwa suka taru suka bi shi zuwa cikin garin. 15Dukan mutanen da suke tare da Yowab kuma suka zo suka kewaye shi cikin Abel-bet-ma'aka. Suka tula ƙasa a jikin garun garin, daidai da tsayinta, waɗansu kuma suna ƙoƙarin rushe garun. 16Sai wata mace mai hikima ta yi kira daga cikin garin, ta ce, “Ji mana! A faɗa wa Yowab, ya zo nan, ina so in yi magana da shi.” 17Da ya zo kusa da ita, sai macen ta ce, “Kai ne Yowab?”
Ya ce, “I, ni ne.”
Ta ce masa, “Ka kasa kunne gare ni.”
Ya ce, “Ina sauraronki.”
18Ta ce, “A dā sukan ce, ‘A nemi shawara a Abel,’ gama a can ake raba gardama. 19Garinmu lafiyayye ne, amintacce ne kuma a cikin Isra'ila. Me ya sa kake so ka hallaka garin? Kana so ka rushe abin da yake na Allah?”
20Yowab ya ce, “Allah ya sawwaƙe! Ba zan lalatar ko in hallakar da birninku ba. 21Ba haka ba ne, ni dai ina neman mutumin ƙasar tudu ta Ifraimu, wanda ake ce da shi Sheba, ɗan Bikri. Shi ne ya tayar wa sarki Dawuda. Shi kaɗai za ku ba ni, ni kuwa zan janye daga garin.”
Macen kuwa ta ce wa Yowab, “To, za a jefar maka kansa ta kan garu.” 22Macen ta tafi wurin dukan mutanen garin da wayo. Su kuwa suka yanke kan Sheba, ɗan Bikri, suka jefa wa Yowab. Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, suka janye daga garin. Kowa ya tafi gidansa. Yowab kuma ya koma Urushalima wurin sarki.
Fādawan Dawuda
(2Sam 8.15-18; 1Tar 18.14-17)
23Yowab shi ne shugaban dukan sojojin Isra'ila, Benaiya, ɗan Yehoyada shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa, wato masu tsaro. 24Adoniram shi ne shugaban aikin gandu, Yehoshafat, ɗan Ahilud, shi ne marubuci. 25Shewa shi ne magatakarda. Zadok da Abiyata su ne firistoci. 26Aira mutumin Yayir shi ne mashawarcin Dawuda.

Currently Selected:

2Sam 20: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in