YouVersion Logo
Search Icon

2Sar 9

9
An Naɗa Yehu Sarkin Isra'ila
1Elisha kuwa ya kirawo ɗaya daga cikin annabawa matasa, ya ce masa, “Ka sha ɗamara, ka ɗauki wannan kurtun mai, ka tafi Ramot-gileyad. 2Sa'ad da ka isa can, sai ka nemi Yehu, ɗan Yehoshafat, wato jikan Nimshi, ka shiga, ka sa ya tashi daga wurin abokansa, ka kai shi cikin ɗaki. 3Sa'an nan ka ɗauki kurtun man, ka zuba masa a ka, ka ce, ‘Ubangiji ya ce ya keɓe ka Sarkin Isra'ila.’ Sa'an nan ka buɗe ƙofa, ka gudu, kada ka tsaya.”
4Sai saurayin nan, annabin, ya tafi Ramot-gileyad. 5Sa'ad da ya isa, sai ga shugabannin sojoji suna taro. Sai ya ce, “Ina da saƙo dominka, ya shugaba.”
Yehu kuwa ya ce, “Wane ne a cikinmu?”
Sai ya ce, “Kai ne, ya shugaba.” 6#1Sar 19.16 Sai Yehu ya tashi ya shiga ɗaki, saurayin kuwa ya zuba masa mai a ka, ya ce, “Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya keɓe ka sarkin jama'arsa, wato Isra'ila. 7Za ka hallaka gidan Ahab, maigidanka, domin in ɗau fansar jinin annabawa bayinsa, da fansar jinin sauran bayin Ubangiji a kan Yezebel. 8Gama dukan gidan Ahab zai hallaka. Zan datse wa Ahab kowane ɗa namiji, bawa ko 'yantacce, cikin Isra'ila. 9Zan mai da gidan Ahab kamar gidan Yeroboam ɗan Nebat, da kuma kamar gidan Ba'asha ɗan Ahija. 10#1Sar 21.23 Karnuka za su cinye Yezebel a cikin Yezreyel, ba wanda zai binne ta.” Sa'an nan ya buɗe ƙofar, ya gudu.
11Da Yehu ya fita zuwa wurin sauran shugabannin, sai suka tambaye shi, “Lafiya kuwa, me ya sa mahaukacin nan ya zo wurinka?”
Sai ya ce musu, “Ai, kun san mutumin da irin maganarsa.”
12Suka ce, “Ba mu sani ba, sai ka faɗa mana.”
Shi kuwa ya ce, “Ya faɗa mini, wai Ubangiji ya ce ya keɓe ni Sarkin Isra'ila.”
13Sai kowane mutum a cikinsu ya yi maza ya tuɓe rigarsa, ya shimfiɗa a kan matakan, sa'an nan suka busa ƙaho, suna cewa, “Yehu ne sarki.”
Yehu Ya Kashe Yehoram Sarkin Isra'ila
14Ta haka Yehu, ɗan Yehoshafat, wato jikan Nimshi, ya tayar wa Yehoram. A lokacin, Yehoram tare da dukan Isra'ila suna tsaron Ramot-gileyad, don kada Hazayel, Sarkin Suriya, ya fāɗa mata. 15Amma sarki Yehoram ya komo Yezreyel, don ya yi jiyyar raunukan da Suriyawa suka yi masa sa'ad da ya yi yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya. Sai Yehu ya ce, “Idan wannan shi ne nufinku, to, kada kowa ya zurare, ya tafi, ya ba da labari a Yezreyel.” 16Sa'an nan Yehu ya hau karusarsa ya tafi Yezreyel, gama a can ne Yehoram yake kwance. Ahaziya Sarkin Yahuza ya gangara don ya gai da Yehoram.
17Mai tsaro kuwa yana tsaye a kan hasumiya a Yezreyel, sai ya hangi rundunar Yehu sa'ad da yake zuwa. Ya ce, “Na ga wata runduna.”
Sai Yehoram ya ce, “Ka aiki wani, ya hau doki, ya tafi ya tarye su, ya tambaye su, ko lafiya.”
18Sai wani mutum ya hau doki ya tafi ya tarye su, ya ce, “Sarki ya ce, lafiya kuwa?”
Sai Yehu ya ce, “Ina ruwanka da lafiya? Kewaya ka bi bayana.”
Mai tsaro kuma ya ce, “Manzo ya kai wurinsu, amma bai komo ba.”
19Ya kuma aiki wani, na biyu, a kan doki, ya je wurinsu ya ce musu, “Sarki ya ce, lafiya kuwa?”
Yehu ya amsa, ya ce, “Ina ruwanka da lafiya? Kewaya ka bi bayana.”
20Mai tsaro ya sāke cewa, “Ya kai wurinsu, amma bai komo ba. Ina ganin sukuwar kamar irin ta Yehu, jikan Nimshi, gama yakan yi sukuwa da hauka.”
21Yehoram kuwa ya ce, “Ku shirya karusa.” Suka shirya masa karusa. Sa'an nan Yehoram Sarkin Isra'ila, da Ahaziya Sarkin Yahuza suka fita, kowa a cikin karusarsa, suka tafi su taryi Yehu. Suka sadu da shi a daidai gonar Nabot mutumin Yezreyel. 22Da Yehoram ya ga Yehu, sai ya ce, “Lafiya dai?”
Yehu ya ce, “Ina fa lafiya, tun da karuwanci da sihirin uwarka, Yezebel, sun yi yawa haka?”
23Yehoram kuwa ya juyar da karusarsa baya, ya gudu, yana ce wa Ahaziya, “Maƙarƙashiya ce, ya Ahaziya!” 24Sai Yehu ya ja bakansa da iyakar ƙarfinsa ya ɗirka wa Yehoram kibiya, ta sha zarar zuciyarsa, sai ya ɓingire cikin karusarsa. 25Yehu ya ce wa Bidkar, “Ka ɗauke shi ka jefar a gonar Nabot mutumin Yezreyel, gama ka tuna sa'ad da ni da kai muke kan dawakai muna biye da Ahab, tsohonsa, yadda Ubangiji ya faɗi wannan magana a kansa cewa, 26#1Sar 21.19 ‘Hakika, kamar yadda jiya na ga jinin Nabot da na 'ya'yansa, ni Ubangiji, zan sāka maka saboda wannan gona.’ Yanzu sai ka ɗauke shi, ka jefar da shi a wannan gona kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”
Yehu Ya Kashe Ahaziya
(2Tar 22.7-9)
27Da Ahaziya Sarkin Yahuza, ya ga haka, sai ya gudu ta hanyar Bet-haggan.Yehu kuwa ya bi shi, ya ce, “Shi ma a harbe shi.” Sai suka harbe shi a cikin karusarsa a hawan Gur, wanda yake kusa da Ibleyam. Sai ya gudu zuwa Magiddo, ya mutu a can. 28Fādawansa suka ɗauke shi a cikin karusar zuwa Urushalima, suka binne shi a kabarinsa tare da kakanninsa a birnin Dawuda.
29Ahaziya ya ci sarautar Yahuza a shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Yehoram ɗan Ahab.
Mutuwar Yezebel
30Da Yezebel ta ji Yehu ya zo Yezreyel, sai ta shafa wa idanunta launi, ta gyara gashin kanta, sa'an nan ta leƙa ta taga. 31Da Yehu ya shiga ƙofar garin, sai ta ce, “Kai Zimri, mai kashe maigidansa, me kake yi a nan?”
32Sai ya ɗaga idanunsa wajen tagar, ya ce, “Wa yake wajena?” Sai babani biyu ko uku suka dube shi, 33shi kuwa ya ce, “Ku wurgo ta ƙasa.” Sai suka wurgo ta ƙasa. Jininta ya fantsama a jikin bangon da jikin dawakan da suka tattake ta. 34Sa'an nan Yehu ya shiga gida, ya ci ya sha, ya ce, “Ku san yadda za ku yi da wannan la'ananniyar mace, ku binne ta, gama ita 'yar sarki ce.” 35Amma da suka tafi don su binne ta, ba su tarar da kome ba sai ƙwaƙwalwa, da ƙafafu, da tafin hannuwanta. 36#1Sar 21.23 Sai suka komo, suka faɗa masa. Sai ya ce musu, “Wannan, ai, faɗar Ubangiji, wadda ya faɗa ta bakin bawansa Iliya Batishbe, ya ce, ‘Karnuka za su cinye naman Yezebel a cikin Yezreyel. 37Gawar Yezebel za ta zama wa ƙasa taki a Yezreyel don kada wani ya iya cewa wannan ita ce Yezebel.’ ”

Currently Selected:

2Sar 9: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in