YouVersion Logo
Search Icon

2Sar 24

24
1 # Irm 25.1-38; Dan 1.1,2 A zamanin Yehoyakim ne Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kawo wa Yahuza yaƙi, Yehoyakim kuwa ya zama baransa har shekara uku daga nan kuma ya tayar masa. 2Ubangiji kuwa ya sa ƙungiyar maharar Kaldiyawa, da ta Suriyawa, da ta Mowabawa, da ta Ammonawa su yi gāba da Yahuza, su hallaka su bisa ga maganar Ubangiji, wadda ya faɗa wa bayinsa annabawa. 3Hakika haka ya faru ga Yahuza bisa ga umarnin Ubangiji domin a kawar da su daga gaban Ubangiji saboda dukan zunubin Manassa da ya aikata, 4saboda kuma marasa laifi waɗanda ya kashe, gama ya cika Urushalima da jinin marasa laifi, Ubangiji kuwa ba zai gafarta wa Manassa ba.
5Sauran ayyukan Yehoyakim da dukan abin da ya yi an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. 6Yehoyakim ya rasu. Ɗansa Yekoniya ya gāji gadon sarautarsa.
7Sarkin Masar kuma bai sāke fitowa daga Masar ba, gama Sarkin Babila ya ƙwace dukan ƙasar da take ta Sarkin Masar, tun daga rafin Masar har zuwa Kogin Yufiretis.
An Kama Sarki Yekoniya da Manya na Yahuza
(2Tar 36.9-10)
8Yekoniya yana da shekara goma sha takwas sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Nehushta 'yar Elnatan, mutumin Urushalima. 9Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda tsohonsa ya yi.
10A zamaninsa ne sojojin Nebukadnezzar Sarkin Babila suka zo Urushalima, suka kewaye ta da yaƙi. 11Nebukadnezzar ya zo birnin lokacin da sojojinsa suka kewaye birnin da yaƙi. 12#Irm 22.24-30; 24.1-10; 29.1,2 Sai Yekoniya Sarkin Yahuza ya ba da kansa ga Sarkin Babila shi da tsohuwarsa, da fādawansa da hakimansa. Sarkin Babila ya kama shi yana da shekara takwas da sarautar, 13ya kuma kwashe dukan dukiyar da take cikin Haikalin Ubangiji, da dukiyar da take cikin gidan sarki. Sai ya farfashe tasoshin zinariya da suke cikin Haikalin Ubangiji, waɗanda Sulemanu Sarkin Isra'ila, ya yi. Ya aikata abin da Ubangiji ya riga ya faɗa. 14Nebukadnezzar ya kwashe dukan mutanen Urushalima, da dukan hakimai da dukan jarumawa, da masu sana'a, da maƙera, har sun kai dubu goma (10,000). Ba wanda ya ragu sai dai matalautan ƙasar.
15 # Eze 17.12 Ya tafi da Yekoniya a Babila, shi da tsohuwarsa, da fādawansa, da masu maƙami na ƙasar. 16Sarkin Babila ya kai kamammu Babila, wato jarumawa dubu bakwai (7,000), masu sana'a da maƙera dubu ɗaya (1,000), dukansu ƙarfafa ne, sun isa zuwa yaƙi.
17 # Irm 37.1; Eze 17.13 Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya naɗa Mattaniya ɗan'uwan tsohon Yekoniya sarki a maimakon Yekoniya sa'an nan ya ba shi suna Zadakiya.
Sarki Zadakiya na Yahuza
(2Tar 36.11-12; Irm 52.1-3)
18 # Irm 27.1-22; 28.1-17 Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Sunan tsohuwarsa Hamutal, 'yar Irmiya, mutumin Libna. 19Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda Yehoyakim ya yi. 20#Eze 17.15 Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai da mutanen Urushalima da dukan mutanen Yahuza, sai ya kore su daga gabansa.
Faɗuwar Urushalima
(2Tar 36.13-16; Irm 39.1-7; 52.3-11)
Zadakiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babila.

Currently Selected:

2Sar 24: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in