YouVersion Logo
Search Icon

2Sar 15

15
Sarki Azariya na Yahuza
(2Tar 26.1-23)
1A shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Yerobowam na biyu Sarkin Isra'ila, Azariya ɗan Amaziya Sarkin Yahuza, ya ci sarauta. 2Yana da shekara goma sha shida sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara hamsin da biyu a Urushalima. Sunan tsohuwarsa, Yekoliya ta Urushalima. 3Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda Amaziya, tsohonsa, ya yi. 4Duk da haka ba a kawar da wuraren tsafi na kan tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadayu da ƙona turare a wuraren tsafi na kan tuddai. 5Sai Ubangiji ya buge shi da kuturta, ya kuwa zama kuturu har ran da ya rasu. Ya zauna a wani gida a ware. Sai Yotam ɗansa ya zama wakilin gidan, yana kuma mulkin jama'ar ƙasar.
6Sauran ayyukan Azariya, da dukan abin da ya yi an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. 7#Ish 6.1 Azariya ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda. Yotam ɗansa ya gāji sarautarsa.
Sarki Zakariya na Isra'ila
8A shekara ta talatin da takwas ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Zakariya ɗan Yerobowam na biyu, ya ci sarautar Isra'ila a Samariya wata shida. 9Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda kakanninsa suka yi. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi. 10Shallum ɗan Yabesh ya ƙulla masa maƙarƙashiya, ya buge shi a Ibleyam, ya kashe shi, sa'an nan ya hau gadon sarautarsa.
11Sauran ayyukan da Zakariya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
12 # 2Sar 10.30 Wannan shi ne alkawarin da Ubangiji ya yi wa Yehu, cewa 'ya'yansa maza za su zauna a gadon sarautar Isra'ila har tsara ta huɗu. Haka kuwa ya zama.
Sarki Shallum na Isra'ila
13Shallum ɗan Yabesh ya ci sarauta a shekara ta talatin da tara ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza. Ya yi mulki wata ɗaya a Samariya.
14Menahem ɗan Gadi daga Tirza ya zo Samariya ya bugi Shallum ɗan Yabesh a Samariya, ya kashe shi, ya hau gadon sarautarsa. 15Sauran ayyukan Shallum duk da makircin da ya ƙulla, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 16A lokacin nan sai Menahem ya hallaka Tifsa da dukan waɗanda suke cikinta, da karkararta tun daga Tirza, domin ba su karɓe shi ba, saboda haka ya hallaka ta, ya tsattsage dukan matan da suke da juna biyu.
Sarki Menahem na Isra'ila
17A shekara ta talatin da tara ta sarautar Azariya, Sarkin Yahuza, Menahem ɗan Gadi, ya ci sarautar. Ya yi shekara goma a Samariya. 18Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. A dukan kwanakinsa bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi. 19Tiglatfilesar, mai mulkin Assuriya, ya kawo wa ƙasar yaƙi, Menahem kuwa ya ba Tiglat-filesar talanti dubu (1,000) na azurfa, don dai ya taimake shi yadda sarautarsa za ta kahu sosai. 20Menahem ya karɓi kuɗin daga mutanen Isra'ila, wato daga attajirai. Ya tilasta wa kowannensu ya ba da azurfa hamsin. Saboda haka Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya ya koma ƙasarsa.
21Sauran ayyukan Menahem, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. 22Menahem ya mutu, ɗansa Fekahiya ya gaji sarautarsa.
Sarki Fekahiya na Isra'ila
23A shekara ta hamsin ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Fekahiya ɗan Menahem, ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara biyu. 24Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi. 25Sai shugaban sojojinsa, wato Feka, ɗan Remaliya daga Gileyad, tare da mutum hamsin suka ƙulla maƙarƙashiya, suka kashe Fekahiya tare da Argob da Ariye a Samariya a fādarsa. Da suka kashe shi, sai Feka ya zama sarki.
26Sauran ayyukan Fekahiya, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
Sarki Feka na Isra'ila
27A shekara ta hamsin da biyu ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Feka ɗan Remaliya ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara ashirin. 28Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra'ila su yi zunubi.
29A zamanin Feka Sarkin Isra'ila, sai Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya, ya zo ya ci Iyon, da Abel-bet-ma'aka, da Yanowa, da Kedesh, da Hazor, da Gileyad, da Galili, da dukan ƙasar Naftali. Sa'an nan ya kwashe mutane zuwa bauta a Assuriya.
30Hosheya ɗan Ila kuwa ya ƙulla wa Feka ɗan Remaliya maƙarƙashiya, ya buge shi ya kashe shi, sa'an nan ya ci sarauta a shekara ta ashirin ta sarautar Yotam ɗan Azariya. 31Sauran ayyukan Feka da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
Sarki Yotam na Yahuza
(2Tar 27.1-9)
32A shekara ta biyu ta sarautar Feka ɗan Remaliya Sarkin Isra'ila, Yotam ɗan Azariya Sarkin Yahuza, ya ci sarauta. 33Yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarautar. Ya yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yerusha, 'yar Zadok. 34Yotam ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda tsohonsa, Azariya, ya yi. 35Duk da haka ba a kawar da wuraren tsafi na kan tuddai ba, amma mutane suka yi ta miƙa hadayu da ƙona turare a matsafai na kan tuddai. Shi ne ya gina ƙofa ta bisa ta Haikalin Ubangiji.
36Sauran ayyukan Yotam, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. 37A kwanakin nan Ubangiji ya fara aiken Rezin Sarkin Suriya da Feka ɗan Remaliya su yi yaƙi da Yahuza. 38Yotam ya rasu, aka binne shi a makabartar kakanninsa a birnin kakansa Dawuda. Sai Ahaz ɗansa ya gaji sarautarsa.

Currently Selected:

2Sar 15: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in