2Kor 7
7
1Ya ku ƙaunatattu, tun da aka yi mana waɗannan alkawarai, sai mu tsarkake kanmu daga kowace irin ƙazanta ta jiki ko ta zuci, da bangirma ga Allah mu kamalta a cikin tsarki.
Bulus Ya Yi Farin Ciki saboda Tubar Ikkilisiya
2Ku saki zuciya da mu, ai, ba mu cuci kowa ba, ba mu ɓata kowa ba, ba mu zambaci kowa ba. 3Ba don in sa muku laifi na faɗi haka ba, don dā ma na gaya muku, abin ƙauna kuke a gare mu ƙwarai, ko a mace ko a raye, ba mu rabuwa. 4Na amince da ku ƙwarai, ina kuma taƙama da ku gaya. Zuciyata ta ƙarfafa ƙwarai. Duk da wahalce-wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske.
5 #
2Kor 2.13
Ko a lokacin da muka zo ƙasar Makidoniya ma, ba mu sami shaƙatawa ba, ana ta wahalshe mu ta kowace hanya, a waje ga husuma, a zukatanmu kuma ga fargaba. 6Amma Allah, shi da yake ƙarfafa wa ƙasƙantattu zuciya, sai ya ƙarfafa mana zuciya da zuwan Titus, 7ba kuwa da zuwan Titus kawai ba, har ma a game da ƙarfafa zuciyar nan da ya samu a wurinku, a yayin da ya gaya mana yadda kuke begena, kuna nadama, kuna kuma himmantuwa ga goyan bayana, har ma na ƙara farin ciki ƙwarai. 8Ko da na ɓata muku rai a game da wasiƙar da dā na rubuto muku, ba na baƙin ciki da haka, ko da yake dā kam na yi baƙin ciki, don na lura wasiƙar nan ta ɓata muku rai, ko da yake dai zuwa ɗan lokaci kaɗan ne. 9Amma a yanzu kam, ina farin ciki, ba don kun yi baƙin ciki ba, sai dai don baƙin cikinmu ya sa ku tuba, don kun yi baƙin ciki irin wanda Allah yake so. Saboda haka, ba ku yi hasarar kome a sanadinmu ba. 10Don baƙin ciki irin wanda Allah yake sawa, shi ne yake biyarwa zuwa ga tuba, da kuma samun ceto, ba ya kuma sa “da na sani”. Amma baƙin ciki a kan al'amarin duniya, yakan jawo mutuwa. 11Ku dubi fa irin himmar da baƙin cikin nan, da Allah yake so ya sa a zukatanku, da irin ɗokin da kuka yi na gyara al'amuranku, da irin haushin da kuka ji, da irin tsoron da kuka ji, da irin begen da kuka yi, da irin himmar da kuka yi, da kuma irin niyyarku ta horo. A game da wannan sha'ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi. 12To, ko da yake na rubuto muku wasiƙa, ba musamman a kan wanda ya yi laifin ba ne, ba kuwa a kan wanda aka cutar ba, sai dai domin a bayyana muku a gaban Allah tsananin kula da kuke yi mana. 13Saboda haka ne zukatanmu suka ƙarfafa.
Banda ƙarfafa zukatanmu kuma, har wa yau mun ƙara farin ciki ƙwarai, saboda farin cikin Titus, don dukanku kun wartsakar da shi. 14Don ko da na gaya masa cewa, ina 'yar taƙama da ku, ban kunyata ba. Kamar yadda duk abin da muka gaya muku gaskiya ne, haka kuma taƙamarmu da ku a idon Titus ma ta zama gaskiya. 15Ransa kuma yana a gare ku fiye da dā ƙwarai, duk sa'ad da yake tunawa da biyayyarku, ku duka, da kuma yadda kuka yi na'am da shi a cikin halin bangirma tare da matsananciyar kula. 16Ina farin ciki ne don na amince da ku ƙwarai da gaske.
Currently Selected:
2Kor 7: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979