YouVersion Logo
Search Icon

2Kor 13

13
Kashedi da Gaisuwa
1 # M.Sh 17.6; 19.15 Wannan shi ne zai zama zuwana na uku a gare ku. Lalle ne kuwa a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku. 2Na gargaɗi waɗanda suka yi zunubi a dā, da kuma saura duka, a yanzu kuma da ba na nan ina yi musu gargaɗi, kamar yadda na yi sa'ad da nake nan a zuwana na biyu, cewa in na sāke zuwa ba zan sawwaƙe musu ba. 3In dai nema kuke yi ku tabbata, cewa da izinin Almasihu nake magana, to, ai, shi ba rarrauna ba ne a gare ku, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku. 4Ko da yake an gicciye shi ne da rashin ƙarfi, duk da haka a raye yake ta ikon Allah. Mu ma marasa ƙarfi ne kamarsa, amma a game da al'amuranku da za mu zartar, a raye muke tare da shi, ta ikon Allah.
5Ku jarraba kanku ku gani, ko har yanzu kuna a raye da bangaskiya. Ku riƙa auna kanku. Ashe, ba ku tabbata Almasihu yana a cikinku ba? Sai ko in kun kasa ga gwajin! 6Muna fata ku gane, mu ba mu kāsa ba. 7Amma muna roƙon Allah kada ku yi wani mugun abu, ba don mu mu zama kamar mun ci gwajin kawai ba, sai dai domin ku yi abin da yake daidai, ko da yake za ku ga kamar mun kāsa. 8Domin ba dama mu sāɓa wa gaskiya, sai dai mu bi bayan gaskiyar. 9Gama farin ciki muke yi in muna raunana, ku kuna ƙarfafa. Addu'armu ita ce ku kammala. 10Ina rubuta wannan ne sa'ad da ba na tare da ku, domin sa'ad da na zo, kada ya zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.
11Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, sai wata rana. Ku kammala halinku. Ku kula da roƙona, ku yi zaman lafiya da juna, ku yi zaman salama, Allah mai zartar da ƙauna da salama kuwa zai kasance a tare da ku. 12Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba. 13Dukan tsarkaka suna gaishe ku.
14Alherin Ubangiji Yesu Almasihu, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su tabbata a gare ku duka.

Currently Selected:

2Kor 13: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy