YouVersion Logo
Search Icon

2Tar 35

35
Yosiya Ya Yi Idin Ƙetarewa
(2Sar 23.21-23)
1Yosiya kuwa ya yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji a Urushalima. A rana ta goma sha huɗu ga wata na fari suka yanka ragon Idin Ƙetarewa. 2Ya sa firistoci a matsayinsu, ya ƙarfafa su a hidimar Haikalin Ubangiji. 3Ya kuma faɗa wa Lawiyawa, tsarkakakku na Ubangiji, waɗanda suke koya wa dukan Isra'ila, ya ce, “Ku sa tsattsarkan akwatin alkawari a Haikalin da Sulemanu ɗan Dawuda, Sarkin Isra'ila, ya gina. Ba za ku sāke ɗaukarsa bisa kafaɗunku ba. Yanzu fa sai ku kama hidimar Ubangiji Allahnku da jama'arsa Isra'ila. 4#2Tar 8.14 Ku karkasa kanku bisa ga gidajen kakanninku ƙungiya ƙungiya, ku bi bayanin Dawuda, Sarkin Isra'ila, da na ɗansa Sulemanu. 5Ku tsaya a Wuri Mai Tsarki, bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakannin 'yan'uwanku, waɗanda su ba firistoci ba ne. Kowanne ya sami kashi daga cikin gidan Lawiyawa. 6Ku yanka abin Idin Ƙetarewa, ku tsarkake kanku, ku shirya wa 'yan'uwanku su yi bisa ga maganar Ubangiji ta hannun Musa.”
7Sarki Yosiya fa ya ba da gudunmawar abin yin hadaya ga waɗanda ba firistoci ba, waɗanda suke wurin, raguna da 'yan awaki daga cikin garken tumaki da na awaki, yawansu ya kai dubu talatin (30,000) da kuma bijimai dubu uku (3,000). Waɗannan duk daga mallakar sarki ne. 8Da yardar rai manyan ma'aikatansa, sarakunansa, suka ba da gudunmawa ga jama'ar, da firistoci, da Lawiyawa. Hilkiya, da Zakariya, da Yehiyel, manyan ma'aikatan Haikalin Allah, suka ba firistoci abin yin hadaya don Idin Ƙetarewa, tumaki da awaki dubu biyu da ɗari shida (2,600), da bijimai ɗari uku. 9Konaniya kuma tare da Shemaiya da Netanel, 'yan'uwansa, da Hashabiya, da Yehiyel, da Yozabad, shugabannin Lawiyawa, su suka ba Lawiyawa abin yin hadayar Idin Ƙetarewa, raguna da 'yan awaki dubu biyar (5,000), da bijimai ɗari biyar.
10Sa'ad da aka shirya yin hidimar, firistoci suka tsaya a wurinsu, Lawiyawa kuwa suka tsaya bisa ga ƙungiyoyinsu, yadda sarki ya umarta. 11Sai suka yanka ragon Idin Ƙetarewar. Sa'an nan firistoci suka karɓi jinin daga gare su, suka yayyafa, Lawiyawa kuma suka yi ta fiɗa. 12Sa'an nan suka keɓe hadayu na ƙonawa domin su rarraba bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakanni waɗanda su ba firistoci ba ne, don su miƙa wa Ubangiji kamar yadda aka rubuta a littafin Musa. Haka nan kuma suka yi da bijiman. 13#Fit 12.8,9 Suka gasa ragon hadayar Idin Ƙetarewa bisa ga ka'idar, sai suka dafa tsarkakan hadayu a tukwane, da manyan tukwane, da kwanoni, nan da nan suka kai wa waɗanda ba firistoci ba. 14Daga baya kuma suka shirya wa kansu da firistoci, saboda firistoci, 'ya'yan Haruna, maza, suna ta hidimar miƙa hadayu na ƙonawa, da kuma na kitse, har dare. Don haka Lawiyawa suka shirya wa kansu abinci, suka kuma shirya wa firistoci, 'ya'yan Haruna, maza. 15#1Tar 25.1 Mawaƙa, 'ya'yan Asaf, maza, suna wurinsu bisa ga umarnin Dawuda, da Asaf, da Heman, da kuma Yedutun maigani na sarki, matsaran ƙofofi kuma suna a kowace ƙofa, ba lalle sai su bar wurin hidimarsu gama 'yan'uwansu Lawiyawa sun shirya musu nasu. 16Haka fa aka shirya dukan hidimar Ubangiji a wannan rana, domin su kiyaye Idin Ƙetarewa, domin kuma su miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden Ubangiji, yadda Yosiya sarki ya umarta. 17#Fit 12.1-20Jama'ar Isra'ila waɗanda suke wurin, suka kiyaye Idin Ƙetarewa, da kuma idin abinci marar yisti har kwana bakwai. 18Ba a taɓa yin Idin Ƙetarewa irin wannan ba tun kwanakin annabi Sama'ila, ba wani kuma daga cikin sarakunan Isra'ila da ya kiyaye Idin Ƙetarewa kamar yadda Yosiya ya kiyaye shi tare da firistoci, da Lawiyawa, da dukan mutanen Yahuza da na Isra'ila, waɗanda suke a wurin, da kuma mazaunan Urushalima. 19A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yosiya aka yi Idin Ƙetarewa.
Rasuwar Yosiya
(2Sar 23.28-30)
20Bayan wannan duka, sa'ad da Yosiya ya shirya Haikali, sai Neko Sarkin Masar, ya zo don ya yi yaƙi a Karkemish wadda take a Yufiretis, sai Yosiya ya fito don ya kara da shi. 21Amma Neko ya aika 'yan saƙo su faɗa masa su ce, “Me ya gama mu da juna, ya Sarkin Yahuza? Ban zo in yi yaƙi da kai ba. Na zo ne in yi yaƙi da Sarkin Assuriya! Ka ƙyale ni! Allah ne ya riga ya faɗa mini in hanzarta. Kada ka yi gāba da Allah, wanda yake tare da ni, don kada ya hallaka ka.” 22Duk da haka Yosiya bai yarda ya koma ba, sai ya ɓad da kama don ya yi yaƙi da shi. Bai yarda da magana wadda Allah ya faɗa wa Neko ba, sai suka kama yaƙi a filin Magiddo.
23Maharba suka harbi sarki Yosiya, sai ya ce wa barorinsa, “Ku ɗauke ni ku tafi da ni, gama an yi mini mummunan rauni.” 24Barorinsa kuwa suka ɗauke shi daga cikin karusa, suka sa shi a karusa ta biyu, suka kawo shi Urushalima, sai ya rasu. Aka binne shi a hurumin kakanninsa. Yahuza da Urushalima fa suka yi makoki domin Yosiya.
25Irmiya kuma ya hurta makoki domin Yosiya. Haka nan kuma dukan mawaƙa mata da maza, suka ambaci Yosiya cikin makokinsu har yau. Suka sa waɗannan su zama farali a Isra'ila, ga shi kuma, an rubuta su a Littafin Makoki.
26Sauran ayyukan Yosiya, da kyawawan ayyukansa, waɗanda ya yi bisa ga abin da aka rubuta a Shari'ar Ubangiji, 27ayyukansa na fari da na ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Isra'ila da na Yahuza.

Currently Selected:

2Tar 35: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in