YouVersion Logo
Search Icon

2Tar 25

25
Sarki Amaziya na Yahuza
(2Sar 14.2-6)
1Amaziya yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara ashirin da tara yana mulki a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yehowaddin ta Urushalima. 2Ya aikata abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji, amma bai rasa aikata laifi a zuciyarsa ba. 3Da ya ga mulkin ya kahu a hannunsa sosai, sai ya karkashe fādawa waɗanda suka kashe tsohonsa, sarki Yowash. 4#M.Sh 24.16 Amma bai karkashe 'ya'yansu ba, bisa ga abin da yake a rubuce a Shari'a, wato Attaura ta Musa, inda Ubangiji ya yi umarni cewa, “Ba za a kashe iyaye saboda 'ya'yansu ba, ba za a kuma kashe 'ya'ya saboda iyaye ba, amma mutum zai mutu saboda laifin kansa.”
5Sa'an nan Amaziya ya tattara mazajen Yahuza, ya kasa su bisa ga gidajen kakanninsu, a ƙarƙashin shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, a dukan Yahuza da Biliyaminu. Sai ya tara 'yan shekara ashirin ko fi, ya sami mutum dubu ɗari uku (300,000) ƙarfafa, waɗanda suka isa zuwa yaƙi, wato za su iya riƙon māshi da garkuwa. 6Ya kuma ɗauko sojan haya, mutum dubu ɗari (100,000) jarumawa daga Isra'ila a bakin talanti ɗari na azurfa. 7Amma mutumin Allah ya zo wurinsa ya ce, “Ya sarki, kada ka yarda rundunar sojojin Isra'ila su tafi tare da kai, gama Ubangiji ba ya tare da Isra'ila, wato da dukan Ifraimawan nan. 8Amma idan ka zaci ta wannan hanya ce za ka zama da ƙarfi don yaƙi, Allah zai kā da kai a gaban maƙiyi, gama Allah yana da iko ya yi taimako, ko kuwa ya ƙi.”
9Amaziya kuwa ya ce wa annabin Allah, “To, me za mu yi yanzu game da azurfar da muka ba sojojin Isra'ila?”
Sai annabin Allah ya amsa ya ce, “Ubangiji yana da iko ya ba ka fiye da haka.” 10Sai Amaziya ya sallami rundunar sojojin da suka zo daga Ifraimu, su koma gida. Sai suka yi fushi da Yahuza ƙwarai suka koma gida cike da hasala mai zafi.
11Amma Amaziya ya yi ƙarfin hali ya shugabanci jama'arsa, suka tafi Kwarin Gishiri, suka karkashe mutanen Seyir dubu goma (10,000). 12Mutanen Yahuza kuma suka kama waɗansu mutum dubu goma (10,000) da rai, suka kai su a ƙwanƙolin dutse, suka yi ta tunkuɗa su ƙasa daga ƙwanƙolin dutsen, duka suka yi kaca-kaca.
13Amma sojojin rundunar da Amaziya ya sallama, bai yarda su tafi yaƙi tare da shi ba, suka faɗa wa biranen Yahuza da yaƙi, tun daga Samariya har zuwa Bet-horon, suka kashe mutum dubu uku (3,000), a cikinsu suka kwashe ganima mai yawan gaske.
14Da Amaziya ya komo daga kisan Edomawa, sai ya kwaso gumakan mutanen Seyir, ya ajiye su su zama gumakansa, ya yi musu sujada, ya kuma miƙa musu hadaya. 15Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da Amaziya. Ubangiji ya aiki annabi a wurinsa. Annabin ya ce masa, “Don me ka koma ga gumakan da ba su iya ceton jama'arsu daga hannunka ba?”
16Yana magana ke nan, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Ka rufe baki! In kuwa ba haka ba in sa a kashe ka.”
Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.”
Yaƙi da Isra'ila
(2Sar 14.8-20)
17Sa'an nan Amaziya Sarkin Yahuza, ya yi shawara ya aika wa Yehowash ɗan Yehowahaz ɗan Yehu, Sarkin Isra'ila, ya ce, “Ka zo mu gabza da juna fuska da fuska.”
18Yehowash Sarkin Isra'ila fa ya aika wa Amaziya Sarkin Yahuza, da amsa ya ce, “Wata ƙaya ce a Lebanon, ta aika wa itacen al'ul na Lebanon cewa, ‘Ka ba ɗana 'yarka aure,’ sai wani naman jeji na Lebanon da yake wucewa, ya tattake ƙayar. 19Ka ce, ga shi, ka ci Edom, zuciyarka ta sa ka fāriya. Amma yanzu sai ka yi zamanka, don me ka tsokano wahalar da za ta kā da kai, da kai da Yahuza tare da kai?”
20Amma Amaziya ya ƙi ji, gama al'amarin daga wurin Allah yake, domin ya bashe su a hannun maƙiyansu, saboda sun koma ga gumakan Edom. 21Sarkin Isra'ila kuwa ya haura, da shi da Amaziya Sarkin Yahuza, suka gabza da juna fuska da fuska a Bet-shemesh, wadda take a ƙasar Yahuza. 22Sai Isra'ila ya runtumi Yahuza, kowane mutum ya gudu zuwa gidansa. 23Yehowash Sarkin Isra'ila, ya kama Amaziya Sarkin Yahuza ɗan Yowash, wato jikan Ahaziya, a Bet-shemesh, ya kawo shi Urushalima. Ya rushe garun Urushalima har tsawon kamu ɗari huɗu, tun daga Ƙofar Ifraimu har zuwa Ƙofar Kusurwa, 24sai ya kwashe dukan zinariya da azurfa, da dukan tukwane da tasoshi da aka samu a Haikalin Allah, waɗanda iyalin Obededom suke tsaro, da kaya masu daraja na gidan sarki, da waɗanda aka kamo cikin yaƙi, ya kawo Samariya.
25Sarki Amaziya ɗan Yowash, Sarkin Yahuza, ya rayu shekara goma sha biyar bayan rasuwar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra'ila. 26Sauran ayyukan Amaziya, daga farko har ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuza da na Isra'ila. 27Daga lokacin da Amaziya ya bar bin Ubangiji, sai suka shirya masa maƙarƙashiya a Urushalima, amma ya gudu zuwa Lakish, sai suka sa a bi shi zuwa Lakish, a can suka kashe shi. 28Sai suka kawo shi a bisa dawakai, suka binne shi tare da kakanninsa a birnin Dawuda.

Currently Selected:

2Tar 25: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in