2Tar 11
11
Annabcin Shemaiya
(1Sar 12.21-24)
1Sa'ad da Rehobowam ya kai Urushalima, sai ya tattara zaɓaɓɓun mayaƙa, mutum dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) daga cikin jama'ar Yahuza da ta Biliyaminu don su yi yaƙi da Isra'ila, su komo wa Rehobowam da mulki. 2Sai Ubangiji ya yi magana da Shemaiya, mutumin Allah, ya ce, 3“Ka faɗa wa Rehobowam ɗan Sulemanu, Sarkin Yahuza, da dukan Isra'ilawa da suke a Yahuza da Biliyaminu, ka ce, 4‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, kada ku yi yaƙi da 'yan'uwanku, kowa ya komo alfarwarsa, gama wannan al'amari daga gare ni yake.’ ” Suka kuwa ji maganar Ubangiji, suka koma, ba su tafi yaƙi da Yerobowam ba.
Rehobowam Ya Arzuta
5Rehobowam ya zauna a Urushalima, ya kuwa gina birane masu kagara a Yehuza. 6Ya gina Baitalami, da Itam, da Tekowa, 7da Bet-zur, da Soko, da Adullam, 8da Gat, da Maresha, da Zif, 9da Adorayim, da Lakish, da Azeka, 10da Zora, da Ayalon, da Hebron. Waɗannan su ne birane masu kagara a Yahuza da Biliyaminu. 11Ya kuma ƙara ƙarfin kagaran, ya sa sarakunan yaƙi a cikinsu. Ya tara abinci, da mai, da ruwan inabi a cikinsu. 12Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen nan, ya ƙara musu ƙarfi ƙwarai. Haka ya riƙe Yahuza da Biliyaminu.
Firistoci da Lawiyawa sun Zo Yahuza
13Firistoci da Lawiyawa da suke a dukan Isra'ila kuwa suka komo gare shi daga dukan wuraren da suke. 14Sai Lawiyawa suka bar makiyayarsu da dukiyarsu, suka koma Yahuza da Urushalima, saboda Yerobowam da 'ya'yansa maza sun hana su yi hidimarsu ta firistocin Ubangiji. 15#1Sar 12.31 Sai Yerobowam ya naɗa firistoci don masujadansa, saboda siffofin bunsurai, da na maruƙa, waɗanda ya yi. 16Amma su waɗanda zuciyarsu take ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, daga kowace kabilar Isra'ila, sukan bi Lawiyawa zuwa Urushalima domin su miƙa hadaya ga Ubangiji, Allah na kakanninsu. 17Sai suka ƙarfafa mulkin Yahuza, suka tsare mutuncin Rehobowam ɗan Sulemanu har shekara uku. Suka yi shekara uku suna tafiya a tafarkin Sulemanu.
Iyalin Rehobowam
18Rehobowam kuwa ya auri Mahalat 'yar Yeremot ɗan Dawuda, wadda Abihail 'yar Eliyab ɗan Yesse ta haifa. 19Mahalat ta haifa masa 'ya'ya maza, su ne Yewush, da Shemariya, da Zaham. 20Banda Mahalat kuma, sai ya auri Ma'aka 'yar Absalom, wadda ta haifa masa Abaija, da Attai, da Ziza, da kuma Shelomit. 21Rehobowam ya fi ƙaunar Ma'aka, 'yar Absalom, fiye da dukan matansa, da ƙwaraƙwaransa. Yana kuwa da matan aure goma sha takwas, da ƙwaraƙwarai sittin. 'Ya'yan da ya haifa maza ashirin da takwas ne, 'ya'ya mata kuwa sittin. 22Sai Rehobowam ya zaɓi Abaija ɗan Ma'aka, ya zama shugaban 'yan'uwansa, gama nufinsa ya zama sarki. 23Sai ya yi hikima ya rarraba waɗansu 'ya'yansa maza ko'ina cikin gundumomin ƙasar Yahuza da ta Biliyaminu, a dukan birane masu kagara, ya tanada musu abinci a yalwace. Ya kuma samo musu mata masu yawan gaske.
Currently Selected:
2Tar 11: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979