YouVersion Logo
Search Icon

1Sam 8

8
Isra'ilawa Sun Roƙa A Naɗa musu Sarki
1Da Sama'ila ya tsufa, sai ya naɗa 'ya'yansa maza su zama alƙalan Isra'ila. 2Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyun kuma Abaija. Su ne alƙalai a cikin Biyer-sheba. 3Amma 'ya'yansa ba su bi gurbin mahaifinsu ba, amma suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi, suka yi ta cin hanci, suka danne gaskiya.
4Dukan shugabannin Isra'ila kuwa suka tattaru, suka tafi wurin Sama'ila a Rama, 5#M.Sh 17.14 suka ce masa, “Ga shi, ka tsufa, ga kuma 'ya'yanka ba su bi gurbinka ba, yanzu dai sai ka naɗa mana sarki wanda zai yi mulkinmu kamar sauran ƙasashe.” 6Amma Sama'ila bai ji daɗin roƙonsu ba, na a naɗa musu sarki, saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji.
7Ubangiji kuwa ya ce masa, “Sai ka kasa kunne ga dukan abin da suka faɗa maka, gama ba kai suka ƙi ba, amma ni suka ƙi da zama sarkinsu. 8Irin abubuwan da suke yi maka, irinsu ne suka yi mini tun daga ranar da na fito da su daga Masar har wa yau, sun ƙi ni, suka yi ta bauta wa gumaka. 9Yanzu dai sai ka saurari maganarsu kurum, amma ka faɗakar da su sosai da sosai, ka kuma nuna musu irin halin sarkin da zai sarauce su.”
10Sama'ila kuwa ya faɗa wa mutanen da suke roƙo ya naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa. 11Ya ce musu, “Ga irin halin sarkin da zai sarauce ku, zai sa 'ya'yanku maza su zama sojojinsa, waɗansunsu za su yi aiki da karusan yaƙinsa, waɗansu su zama mahayan dawakansa, da masu kai hari musamman. 12Waɗansu kuma zai sa su zama shugabannin mutum dubu dubu da na hamsin hamsin. 'Ya'yanku ne za su riƙa yi masa noma da girbi, su ƙera masa kayayyakin yaƙi da na karusansa. 13Zai sa 'ya'yanku mata yin aikin turare, da dafe-dafe, da toye-toye. 14Zai ƙwace gonakinku mafi kyau, da gonakinku na inabi, da gonakinku na zaitun, ya ba fādawansa. 15Zai kuma karɓi ushirin hatsinku da na inabinku ya ba shugabannin fādarsa da sauran fādawansa. 16Zai ƙwace bayinku mata da maza, da mafi kyau na shanunku da jakunanku, domin su riƙa yi masa aiki. 17Zai kuma karɓi ushirin dabbobinku. Za ku zama barorinsa. 18A lokacin za ku yi kuka saboda sarkin da kuka zaɓar wa kanku, amma Ubangiji ba zai kasa kunne ga kukanku ba.”
19Amma mutane suka ƙi jin abin da Sama'ila ya faɗa musu, sai suka ce, “Duk da haka dai, muna so sarki ya sarauce mu, 20don mu ma mu zama kamar sauran ƙasashe, mu sami sarki wanda zai sarauce mu, ya shugabance mu zuwa yaƙe-yaƙe.” 21Sa'ad da Sama'ila ya ji dukan abin da mutanen suka faɗa, sai ya mayar wa Ubangiji.
22Ubangiji kuwa ya ce wa Sama'ila, “Ka yarda da abin da suka ce, ka naɗa musu sarki.”
Sai Sama'ila ya ce wa mutanen Isra'ila, “Kowa ya koma gida.”

Currently Selected:

1Sam 8: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in