1Sam 28
28
1A kwanakin nan Filistiyawa suka tattara sojojinsu don su yi yaƙi da Isra'ilawa. Akish kuwa ya ce wa Dawuda, “Sai ka sani fa, kai da mutanenka za ku tafi tare da ni da sojojina.”
2Sai Dawuda ya ce, “Za ka ga abin da baranka zai yi.”
Akish ya ce wa Dawuda, “Da kyau, zan sa ka cikin zaunannun jarumawan da suke kāre ni.”
Saul Ya Tafi wurin Mai Duba
3 #
1Sam 25.1
#
L.Fir 20.27; M.Sh 18.10,11 Sama'ila ya riga ya rasu, dukan Isra'ilawa kuwa suka yi makoki dominsa, suka binne shi a garinsu, wato Rama. Saul kuma ya riga ya kori masu duba da masu maita daga ƙasar.
4Filistiyawa suka kafa sansaninsu a Shunem. Saul ya tattara Isra'ilawa, su ma suka kafa sansaninsu a Gilbowa. 5Da Saul ya ga rundunar yaƙin Filistiyawa, sai ya tsorata, ya yi rawar jiki ƙwarai. 6#L.Ƙid 27.21 Saul kuwa ya yi tambaya ga Ubangiji, Ubangiji bai amsa masa ba, ko ta mafarkai, ko ta Urim, ko ta annabawa. 7Sai ya ce wa barorinsa, “Ku nemo mini wata mace mai duba domin in tafi wurinta in yi tambaya.”
Barorinsa suka ce masa, “Ai, akwai wata mai duba a Endor.”
8Sai Saul ya ɓad da kama, ya sa waɗansu tufafi. Shi da waɗansu mutum biyu suka tafi wurin matar da dare. Ya ce mata, “Ina roƙonki ki duba mini ta hanyar sihiri. Ki hawar mini da duk wanda zan faɗa miki.”
9Matar ta ce masa, “Hakika ka san abin da sarki Saul ya yi, yadda ya karkashe masu duba da masu maita a ƙasar. Me ya sa kake ƙoƙarin kafa mini tarko, don ka sa a kashe ni?”
10Saul ya rantse mata da Ubangiji, ya ce, “Hakika, ba za a hukunta ki saboda wannan ba.”
11Sai matar ta ce, “Wa kake so in hawar maka?”
Ya ce, “Ki hawar mini da Sama'ila.”
12Da matar ta ga Sama'ila, sai ta fasa ƙara, ta ce wa Saul, “Don me ka ruɗe ni, ashe, kai ne sarki Saul?”
13Sarki kuwa ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, me kike gani?”
Ta ce masa, “Na ga wani allah yana fitowa daga ƙasa.”
14Ya ce mata, “Yaya kamanninsa yake?”
Ta ce, “Wani tsoho ne yake hawowa, yana naɗe da alkyabba.”
Saul ya gane Sama'ila ne, sai ya sunkuyar da kai, ya durƙusa har ƙasa da bangirma.
15Sai Sama'ila ya ce wa Saul, “Don me ka dame ni, ka hawar da ni?”
Saul ya ce, “Ina cikin babbar wahala, gama Filistiyawa suna yaƙi da ni, Allah kuma ya rabu da ni, ya ƙi amsa mini ko ta wurin annabawa ko ta mafarkai, saboda haka na kira ka, ka faɗa mini abin da zan yi.”
16Sai Sama'ila ya ce masa, “Don me za ka tambaye ni, tun da yake Ubangiji ya rabu da kai, ya zama magabcinka? 17#1Sam 15.28 Ai, abin da Ubangiji ya faɗa mini a kanka, shi ne ya cika, gama Ubangiji ya fizge mulki daga hannunka, ya ba maƙwabcinka Dawuda. 18#1Sam 15.3-9 Domin ba ka bi maganar Ubangiji ba, ba ka zartar da hukuncinsa mai zafi a kan Amalekawa ba, saboda haka Ubangiji ya yi maka haka yau. 19Banda haka kuma Ubangiji zai ba da Isra'ilawa tare da kai a hannun Filistiyawa. Gobe, da kai da 'ya'yanka maza za ku kasance tare da ni. Ubangiji zai ba da rundunar yaƙin Isra'ila a hannun Filistiyawa.”
20Da jin maganar Sama'ila sai Saul ya faɗi ƙasa warwar. Tsoro ya kama shi ƙwarai. Ba shi kuma da ƙarfi domin bai ci kome dukan yini da dukan dare ba. 21Sai matar ta zo wurin Saul, da ta ga ya tsorata, sai ta ce masa, “Baiwarka ta yi kasai da ranta, ta kuwa kasa kunne gare ka. 22To, kai ma ka kasa kunne ga baiwarka. Bari in ba ka abinci, ka ci don ka sami ƙarfin tafiya.”
23Sai ya ƙi, ya ce, “Ba zan ci abinci ba.” Sai da barorinsa da matar suka roƙe shi, sa'an nan ya ji maganarsu, ya tashi daga ƙasa, ya zauna a bakin gado. 24Matar kuwa ta yi hanzari ta yanka turkakken maraƙinta, ta ɗauki gari ta kwaɓa, ta toya abinci marar yisti da shi. 25Sa'an nan ta kawo wa Saul da barorinsa, suka ci, sa'an nan suka tashi suka tafi da daren nan.
Currently Selected:
1Sam 28: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979