1Bit 3:15-16
1Bit 3:15-16 HAU
Sai dai ku girmama Almasihu a zukatanku da hakikancewa, shi Ubangiji ne. Kullum ku zauna a shirye ku ba da amsa ga duk wanda ya tambaye ku dalilin begen nan naku, amma fa da tawali'u da bangirma. Ku kuma kasance da lamiri mai kyau, don in an zage ku, waɗanda suka kushe kyakkyawan halinku na bin Almasihu su kunyata.










