YouVersion Logo
Search Icon

1Sar 7

7
Fādar Sulemanu
1Sulemanu ya yi shekara goma sha uku yana gina gidansa kafin ya gama shi duka.
2Ya kuma gina wani ɗaki da katakai daga kurmin Lebanon, tsawonsa kamu ɗari, faɗinsa kuma kamu hamsin, tsayinsa kuwa kamu talatin, a bisa jeri huɗu na ginshiƙan itacen al'ul. Aka shimfiɗa katakan itacen al'ul a bisa ginshiƙan. 3Aka rufe shi da katakan al'ul a bisa ɗakuna arba'in da biyar da suke gefe, waɗanda suke bisa ginshiƙai. Ɗakuna goma sha biyar a kowane jeri har jeri uku. 4Aka kuma yi tagogi masu sandunan ƙarfe, jeri uku, kowace taga tana daura da 'yar'uwarta, har jeri uku. 5Dukan ƙofofin da madogaransu murabba'i ne, taga kuma tana daura da 'yar'uwarta har jeri uku.
6Ya yi babban shirayi mai ginshiƙai, tsawonsa kamu hamsin, faɗinsa kamu talatin. Akwai kuma wani shirayi mai ginshiƙai a gabansa. 7Ya kuma gina shirayi ta sarauta inda zai riƙa yin shari'a, ya rufe dukan daɓenta da itacen al'ul.
8 # 1Sar 3.1 Ya gina gidan da zai zauna a farfajiya na ciki, wajen shirayi. ya kuma gina wa matarsa, 'yar Fir'auna, gida irin wannan.
9Aikin gine-ginen nan, an yi shi da duwatsu masu tamani tun daga tushen har zuwa rufin. Sai da aka auna duwatsun sa'an nan aka yanka su da zarto, ciki da baya daidai da juna. 10An kafa harsashin ginin da manyan duwatsu masu tsada, waɗansu kamu takwas waɗansu goma. 11Daga sama kuma akwai duwatsu masu tsada waɗanda aka yanka su bisa ga ma'auni, da kuma itacen al'ul. 12Babbar farfajiyar fāda, da filin Haikali na ciki da shirayin Haikalin yana da bangaye da jerin katakan al'ul domin kowane jeri uku na yankakkun duwatsu.
Aikin Huram
(2Tar 2.13-14; 3.15—5.1)
13Sarki Sulemanu kuwa ya aika a kawo Huram daga Taya, gwanin aikin tagulla ne. 14Shi ɗan wata mata ne daga kabilar Naftali wadda mijinta ya rasu. Huram mutumin Taya ne, maƙerin tagulla. Yana da hikima, da fahimi, da fasaha na iya yin kowane irin aiki da tagulla. Ya kuwa amsa kiran sarki Sulemanu, ya zo ya yi masa dukan aikinsa.
15Ya kuwa yi ginshiƙi biyu na zubi da tagulla. Kowane ginshiƙi tsayinsa kamu goma sha takwas ne, da guru mai kamu goma sha biyu kewaye da shi. 16Ya kuma yi dajiya biyu ta zubi da tagulla don a sa a kan ginshiƙan. Tsayin kowace dajiya kamu biyar ne. 17Ya yi wa kowace dajiya da take kan ginshiƙan ragogi da tukakkun sarƙoƙi. Kowace dajiya tana da guda bakwai. 18Ta haka ya yi ginshiƙai jeri biyu kewaye da raga don rufe dajiya wadda take da siffofin rumman, haka kuma ya yi wa ɗaya dajiyar.
19Dajiyar da take kan ginshiƙai na cikin shirayin an yi su da fasalin bi-rana kamu huɗu huɗu. 20Dajiyar tana kan ginshiƙan nan biyu kusa da wani abu mai kama da gammo, wanda yake kusa da ragar. Akwai jeri biyu na siffofin rumman guda ɗari biyu a kewaye da dajiyar.
21Ya kafa ginshiƙan a shirayin Haikalin. Ya kafa ginshiƙi ɗaya a wajen dama, ya sa masa suna, Yakin, wato Allah ya kafa. Ya kafa ɗaya ginshiƙin a wajen hagu, ya sa masa suna Bo'aza, wato da ƙarfin Allah. 22A bisa kawunan ginshiƙan akwai dajiya masu fasalin bi-rana. Haka aka gama aikin ginshiƙan.
23Huram kuma ya yi kewayayyiyar babbar kwatarniya ta zubi da tagulla. Faɗinta kamu goma ne, tsayinta kuwa kamu biyar, da'irarta kuma kamu talatin ne. 24Akwai goruna kewaye da gefensa. Gora goma a kowane kamu ɗaya. Suka kewaye kwatarniya. Gorunan jeri biyu ne, an yi zubinsu haɗe da kwatarniyar. 25Aka ɗora ta a kan siffofin bijimai goma sha biyu. Siffofin bijimai uku suna fuskantar gabas, uku kuma suna fuskantar yamma, uku suna fuskantar kudu, uku kuma suna fuskantar arewa. An ɗora kwatarniya a kansu. Gindinsu duka na wajen ciki. 26Kaurin kwatarniya ya kai taƙin hannu guda. An yi gefenta kamar finjali, kamar kuma furen bi-rana. Takan ci garwa dubu biyu.
27Ya kuma yi dakali goma da tagulla. Kowane dakali tsawonsa kamu huɗu, faɗinsa kuma kamu huɗu, tsayinsa kuwa kamu uku ne. 28Yadda aka yi dakalan ke nan, dakalan suna da sassa, sassan kuma suna da mahaɗai. 29Aka zana hotunan zakoki, da na bijimai, da na kerubobi a kan sassan. A kan mahaɗan kuma akwai gammo, aka zana hotunan furanni a ƙarƙashin zakokin da bijiman. 30Kowane dakali yana da ƙafa huɗu na tagulla kamar na karusa, da sandunan tagulla don sa kwatarniya. A kusurwoyin akwai abubuwa na zubi don tallabar kwatarniya. An zana furanni a kowane gefensu. 31Bakinsa daga cikin dajiyar ya yi sama kamu guda. Bakin da'ira ne kamar fasalin gammo, kamu ɗaya da rabi. Akwai zāne-zāne a bakin. Sassan murabba'i ne, ba da'ira ba. 32Ƙafafu huɗu ɗin, suna ƙarƙashin sassan. Sandunan ƙafafun a haɗe suke da dakalan. Tsayin kowace ƙafa kuwa kamu ɗaya da rabi ne. 33Ƙafafun suna kama da ƙafafun karusa. Sandunan ƙafafun, da gyaffansu, da kome na ƙafafun duka na zubi ne. 34Akwai ginshiƙi huɗu daga ƙarƙashin kowane dakali. Ginshiƙan suna haɗe da dakalan. 35Akwai wani abu kamar gammo mai tsayi rabin kamu a kan dakalin. Ginshiƙan kuma da sassan a haɗe suke da dakalin. 36Ya zana siffofin kerubobi, da na zakoki, da na itatuwan dabino a jikin ginshiƙan da sassan a duk inda ya ga akwai fili. Ya kuma zana furanni kewaye da su.
37Haka aka yi dakalai, dukansu iri ɗaya ne, girmansu da fasalinsu kuma iri ɗaya ne.
38 # Fit 30.17-21 Ya kuma yi daruna na tagulla guda goma. Kowane daro yana cin misalin garwa tamanin. Kowane daro kamu huɗu ne. Kowane dakali yana da daro ɗaya. 39Ya kafa dakali biyar a gefen dama na Haikalin, ya kuma kafa biyar a gefen hagu na Haikalin. Ya kuma sa kwatarniya na zubi a gefen dama na Haikalin, wajen kusurwar gabas maso kudu.
Jerin Kayan Haikali
40-45Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe da manyan cokula, da daruna. Haka Huram ya gama dukan aikin da ya yi wa Sulemanu a cikin Haikalin Ubangiji. Ga abin da ya yi.
ginshiƙai biyu
dajiya da take a kawunan ginshiƙan
raga biyu don rufe dajiyar da take a
kawunan ginshiƙai
siffofin rumman ɗari huɗu domin
raga biyu ɗin, da jeri biyu na
siffofin rumman domin kowace
raga don a rufe dajiyar da take a
kawunan ginshiƙan
dakalai goma
daruna goma a kan dakalan
kwatarniya ɗaya
siffofin bijimai guda goma sha biyu
da kwatarniya take zaune a kai,
tukwanen ƙarfe, da manyan cokula,
da kwanoni.
Dukan kayayyakin aiki a cikin Haikalin Ubangiji waɗanda Huram ya yi wa sarki Sulemanu, an yi su ne da gogaggiyar tagulla. 46Sarki ya sa a yi zubinsu a filin Urdun a ƙasar yumɓun da yake tsakanin Sukkot da Zaretan. 47Sulemanu bai auna nauyin kayayyakin aikin ba domin sun cika yawa. Ba a kuma san nauyin tagullar ba.
48-50 # Fit 30.1-3; Fit 25.23-30 # Fit 25.31-40 Sulemanu ya yi dukan kayayyakin aikin da suke na Haikalin Ubangiji.
bagaden zinariya
teburin zinariya inda ake ajiye
gurasar ajiyewa
alkuki na zinariya guda biyar a gefen
dama, biyar kuma a gefen hagu a
gaban Wuri Mafi Tsarki na can ciki
furanni
fitilu
arautaki
finjalai na zinariya
hantsuka
daruna
cokula
farantan wuta na zinariya tsantsa
almanani na zinariya domin ƙofofin
ɗaki na can cikin Haikali, wato
Wuri Mafi Tsarki, da ƙofofin Haikalin.
51 # 2Sam 8.11; 1Tar 18.11 Haka sarki Sulemanu ya gama dukan aikin Haikalin Ubangiji. Sai ya kawo abubuwan da tsohonsa Dawuda ya keɓe, wato azurfa, da zinariya, da kayayyakin aiki, ya ajiye su cikin taskokin Haikalin Ubangiji.

Currently Selected:

1Sar 7: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in