1Sar 4
4
Fādawan Sulemanu
1Sarki Sulemanu shi ne sarkin dukan Isra'ila, 2-6waɗannan kuma su ne manyan fādawansa,
Azariya ɗan Zadok shi ne firist.
Elihoref da Ahija 'ya'yan Seraiya,
maza, su ne magatakarda.
Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne mai
lura da takardu.
Benaiya ɗan Yehoyada shi ne
shugaban sojoji.
Zadok da Abiyata su ne firistoci.
Azariya ɗan Natan shi ne shugaban
hakimai.
Zabud ɗan Natan shi ne mashawarcin
sarki da abokinsa.
Ahishar shi ne mai lura da bayin fāda.
Adoniram ɗan Abda, shi ne mai lura
da aikin gandu.
7Sulemanu kuma ya naɗa mutum goma sha biyu a lardunan Isra'ila. Su ne za su tanaji abinci daga lardunansu domin sarki da iyalinsa. Kowane hakimi yakan kawo abinci wata guda a shekara. 8-19Waɗannan su ne hakimai, da kuma lardunan da suke aiki.
Ben-hur yana a ƙasar tudu ta Ifraimu.
Ben-deker shi ne mai lura da biranen
Makaz, da Shalim, da Bet-shemesh,
da Elon-bet-hanan.
Ben-hesed shi ne mai lura da Arubot,
da Soko, da dukan ƙasar Hefer.
Ben-abinadab shi ne mai lura da
dukan jihar Dor, ya auri Tafat
'yar Sulemanu.
Ba'ana ɗan Ahilud shi ne mai lura da
biranen Ta'anak da Magiddo, da
dukan jihar Bet-sheyan, kusa da
garin Zaretan, kudu da garin
Yezreyel, har zuwa birnin Abel
mehola da birnin Yokmeyam.
Ben-geber shi ne mai fura da birnin
Ramot-gileyad, da ƙauyukan
Yayir da Manassa, waɗanda suke a
Gileyad, da kuma yankin Argob,
wanda yake a Bashan, duka dai
akwai manyan garuruwa sittin
masu garu da ƙyamare na tagulla.
Abinadab ɗan Iddo shi ne mai lura
da birnin Mahanayim.
Ahimawaz shi ne mai lura da Naftali,
ya auri Basemat 'yar Sulemanu.
Ba'ana ɗan Hushai shi ne mai lura
da Ashiru da garin Beyalot.
Jehoshafat ɗan Faruwa shi ne mai
lura da Issaka.
Shimai ɗan Ila shi ne mai lura da
ƙasar Biliyaminu.
Geber ɗan Uri shi ne mai lura da
jihar Gileyad wadda Sihon Sarkin
Amoriyawa, da Og Sarkin Bashan,
suka mallaka.
Bayan waɗannan sha biyu akwai hakimi ɗaya da yake kan ƙasar Yahuza.
Hikimar Sulemanu da Wadatarsa
20Mutanen Yahuza da na Isra'ila suka yi yawa kamar yashi a bakin teku. Suka ci, suka sha, suka yi murna. 21#Far 15.18; 2Tar 9.26 Sulemanu ya sarauci dukan mulkoki tun daga Kogin Yufiretis a gabas, har zuwa ƙasar Filistiyawa a yamma, daga kudu kuma har zuwa iyakar Masar. Su kuwa suka yi ta kawo wa Sulemanu harajinsu, ya kuwa mallake su dukan kwanakin ransa.
22Abincin gidan Sulemanu na rana ɗaya garwa talatin na lallausan gari ne, da garwa sittin na gari, 23da turkakkun bijimai goma, da shanu ashirin daga makiyaya, da tumaki ɗari banda kishimai, da bareyi, da batsiyoyi, da kaji masu ƙiba.
24Sulemanu ya mallaki dukan ƙasar da yake yamma da Kogin Yufiretis, daga Tifsa har zuwa birnin Gaza. Ya mallaki dukan sarakuna yammacin Yufiretis. Akwai zaman lafiya ko'ina a mulkinsa da ƙasashen maƙwabta. 25Mutanen Yahuza da na Isra'ila suka zauna lafiya tun daga Dan har Biyersheba. Kowa ya yi zamansa a gida dukan kwanakin Sulemanu.
26 #
1Sar 10.26; 2Tar 1.14; 9.25 Sulemanu kuma yana da rumfuna dubu arba'in (40,000) domin dawakan karusansa, da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000). 27Hakiman nan nasa sha biyu, kowa ya kawo wa Sulemanu abinci, duk da waɗanda suke zuwa teburin cin abincin Sulemanu. Kowane hakimi yakan kawo abincin da za a ci na wata guda. Ba su fasa kawowa ba. 28Suka kuma kawo sha'ir da ingirci domin dawakan da suke jan karusai, da sauran dabbobin da suke aiki. Kowanne bisa ga abin da aka sa masa.
29Allah ya ba Sulemanu hikima, da fahimi, da sani, har ba su misaltuwa. 30Hikimar Sulemanu ta fi ta dukan mutanen gabas, ko masu hikima na Masar. 31#Zab 89 Gama ya fi dukan mutane hikima, ya fi Etan Ba'ezrahe, da Heman, da Kalkol, da Darda, 'ya'yan Mahol. Ya shahara a ƙasashen da suke kewaye da shi. 32#K.Mag 1.1; 10.1; 25.1; W.W 1.1 Ya yi karin magana dubu uku, ya kuma yi waƙoƙi fiye da dubu. 33Ya yi magana a kan itatuwa da tsire-tsire tun daga itacen al'ul da yake a Lebanon har zuwa ɗaɗɗoya da take tsirowa a jikin bango. Ya kuma yi magana a kan dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kifaye. 34Sarakuna daga ko'ina a duniya, sun ji labarin hikimarsa, suka kuma aika da mutane don su ji shi.
Currently Selected:
1Sar 4: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979