1Sar 17
17
Iliya Ya yi Annabci Za a yi Fari
1 #
Yak 5.17
Wani annabi mai suna Iliya, mutumin Tishbi a Gileyad, ya ce wa sarki Ahab, “Na rantse da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda nake bauta wa, ba za a yi raɓa ko ruwan sama cikin shekarun nan ba, sai da faɗata.”
2Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Iliya, 3“Ka tashi daga nan ka nufi wajen gabas, ka ɓuya a rafin Kerit, a gabashin Urdun. 4Za ka riƙa samun ruwan sha daga rafin, na kuma umarci hankaki su ciyar da kai a can.”
5Iliya kuwa ya tafi, ya yi yadda Ubangiji ya faɗa, ya tafi ya zauna a rafin Kerit wanda yake gabashin Urdun. 6Hankaki kuma suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da maraice. Yakan kuma sha ruwa daga rafin. 7Da aka jima sai rafin ya ƙafe saboda ba a yin ruwan sama a ƙasar.
Iliya da Mace Gwauruwa a Zarefat
8Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Iliya. 9#Luk 4.25,26 “Tashi ka tafi Zarefat ta Sidon, ka zauna a can. Ga shi, na umarci wata mace wadda mijinta ya rasu ta ciyar da kai.”
10Sai ya tashi, ya tafi Zarefat. Sa'ad da ya isa ƙofar garin, sai ga wata wadda mijinta ya rasu tana tattara itace. Sai ya kira ta, ya ce, “Ki kawo mini ɗan ruwa in sha.” 11Ta juya ta tafi don ta kawo masa ruwan sha ke nan, sai ya sāke kiranta, ya ce, “Ki kuma kawo mini ɗan abinci.”
12Ta ce, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da abinci, sai dai ɗan farin da ya ragu a tukunya, da ɗan man da yake cikin kurtu. Ga shi, ina tattara itacen don in je in shirya shi domin ni da ɗana, mu ci. Shi ke nan, ba sauran wani abu kuma, sai mutuwa.”
13Amma Iliya ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, ki tafi, ki yi yadda kika ce, amma ki fara yi mini 'yar waina, ki kawo mini, sa'an nan ki yi wa kanki da ɗanki. 14Gama Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Garin da yake a tukunyarki ba zai ƙare ba, man da yake a kurtunki kuma ba zai ƙare ba, sai ran da Ubangiji ya sa aka yi ruwan sama a ƙasar.’ ”
15Ta tafi, ta yi yadda Iliya ya ce, dukansu kuwa suka sami isasshen abinci har kwanaki da yawa. 16Garin da yake cikin tukunyar bai ƙare ba, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Iliya.
17Bayan wannan sai ɗan macen, wato ɗan uwargijiyar gidan, ya yi ciwo. Ciwon kuwa ya tsananta har ransa ya fita. 18Sai macen ta ce wa Iliya, “Me ya haɗa ni da kai, ya mutumin Allah? Ka zo don ka nuna wa Allah zunubina, ka zama sanadin mutuwar ɗana?”
19Iliya ya ce mata, “Ki kawo mini ɗanki.” Ya karɓe shi daga wurinta, ya kai shi a bene inda yake kwana. Ya kwantar da shi a gadonsa. 20Sa'an nan ya yi addu'a da gaske ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, don me ka kawo wa gwauruwan nan da nake zaune wurinta masifa, ka aukar wa ɗanta da ajali?” 21#2Sar 4.34,35 Sa'an nan ya kwanta ya miƙe a kan yaron sau uku, ya kuma yi addu'a ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, ka sa ran yaron nan ya komo cikinsa.” 22Ubangiji kuwa ya amsa wa Iliya, ran yaron ya komo cikinsa, sai ya farfaɗo.
23Iliya ya ɗauki yaron ya sauko da shi daga soro, ya kai shi cikin gida, ya ba uwar. Ya ce mata, “Ki gani, ɗanki yana da rai.”
24Sai macen ta ce wa Iliya, “Yanzu na sani kai mutumin Allah ne, Ubangiji kuwa yana magana ta wurinka.”
Currently Selected:
1Sar 17: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979