YouVersion Logo
Search Icon

1Kor 12

12
Bayebaye na Ruhu
1A yanzu kuma 'yan'uwa, a game da baye-baye na ruhu, ba na so ku rasa sani. 2Kun sani fa a sa'ad da kuke bin al'ummai, an juyar da ku ga bin gumakan nan marasa baki yadda aka ga dama. 3Don haka nake sanar da ku, cewa ba mai magana ta wurin ikon Ruhun Allah sa'an nan ya ce, “Yesu la'ananne ne!” Haka kuma ba mai iya cewa, “Yesu Ubangiji ne,” sai ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
4 # Rom 12.6-8 To, akwai baiwa iri iri, amma Ruhu ɗaya ne. 5Akwai fanni iri iri na ibada, amma Ubangiji ɗaya ne. 6Akwai kuma aiki iri iri, amma Allah ɗaya yake iza kowa ga yin kowannensu. 7An yi wa kowanne baiwa da wani buɗi na Ruhu, don kyautata wa duka. 8Wani an yi masa baiwa da koyar da hikima ta wurin Ruhu, wani kuma da koyar da sani ta wurin wannan Ruhu. 9Wani kuwa an yi masa baiwa da bangaskiya ta wurin Ruhun nan, wani kuma baiwar warkarwa ta wurin Ruhun nan, 10wani kuma yin mu'ujizai, wani kuma annabci, wani kuma baiwar rarrabe ruhu da aljani, wani kuma iya harshe iri iri, wani kuma fassara harsuna. 11Dukan waɗannan Ruhu ɗaya ne da yake iza su, yake kuma rarraba wa ko wannensu yadda ya nufa.
Dukkanmu Gaɓoɓin Jiki Guda Ne
12 # Rom 12.4,5 Wato, kamar yadda jiki yake guda, yake kuma da gaɓoɓi da yawa su gaɓoɓin kuwa ko da yake suna da yawa, jiki guda ne, to, haka ga Almasihu. 13Dukanmu an yi mana baftisma ta wurin Ruhu guda, mu zama jiki guda, Yahudawa ko al'ummai, bayi ko 'ya'ya, dukanmu kuwa an shayar da mu Ruhu guda.
14Jiki ba gaba ɗaya ba ne, gaɓoɓi ne da yawa. 15Da ƙafa za ta ce, “Da yake ni ba hannu ba ce, ai, ni ba gaɓar jiki ba ce,” faɗar haka ba za ta raba ta da zama gaɓar jikin ba. 16Da kuma kunne zai ce, “Da yake ni ba ido ba ne, ai, ni ba gaɓar jiki ba ne,” faɗar haka ba za ta raba shi da zama gaɓar jikin ba. 17Da dukan jiki ido ne, da me za a ji? Da dukan jiki kunne ne, da me za a sansana? 18Amma ga shi, Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowaccensu yadda ya nufa. 19Da dukan jikin gaɓa ɗaya ne, da ina sauran jikin? 20Amma ga shi, akwai gaɓoɓi da yawa, jiki kuwa ɗaya. 21Ba dama ido yă ce wa hannu, “Ba ruwana da kai,” ko kuwa kai yă ce wa ƙafafu, “Ba ruwana da ku.” 22Ba haka yake ba, sai ma gaɓoɓin da ake gani kamar raunana, su ne wajibi, 23gaɓoɓin jiki kuma da ake gani kamar sun kasa sauran daraja, mukan fi ba su martaba. Ta haka gaɓoɓinmu marasa kyan gani, akan ƙara kyautata ganinsu. 24Gaɓoɓinmu masu kyan gani kuwa ba sai an yi musu kome ba. Amma Allah ya harhaɗa jiki, yana ba da mafificiyar martaba ga ƙasƙantacciyar gaɓa, 25kada rashin haɗa kai ya kasance ga jiki, sai dai gaɓoɓin su kula da juna, kula iri ɗaya. 26Ta haka, in wata gaɓa ta ji ciwo, duk sai su ji ciwo tare, in kuwa an yabi wata, duk sai su yi farin ciki tare.
27To, ku jikin Almasihu ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne. 28#Afi 4.11 A cikin ikkilisiya, Allah ya sa waɗansu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa'an nan sai masu yin mu'ujizai, sai masu baiwar warkarwa, da mataimaka, da masu tafiyar da Ikkilisiya, da kuma masu magana da harsuna iri iri. 29Shin, duka manzanni ne? Ko duka annabawa ne? Ko duk masu koyarwa ne? Su duka masu yin mu'ujizai ne? 30Duka ne suke da baiwar warkarwa? Duka ne suke magana da waɗansu harsuna? Ko kuwa duka ne suke fassara? 31Sai dai ku himmantu ga neman mafafitan bayebaye.
Har ma zan nuna muku wata hanya mafificiya nesa.

Currently Selected:

1Kor 12: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in