YouVersion Logo
Search Icon

1Tar 28

28
Dawuda Ya Danƙa Ginin Haikali ga Sulemanu
1Dawuda ya yi umarni a tara dukan shugabannin Isra'ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin ƙungiyoyin da suke bauta wa sarki, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da masu lura da dukan dukiya da dabbobin sarki, da na 'ya'yansa, da fādawa, da manyan sojoji, da jarumawa, a Urushalima.
2 # 2Sam 7.1-16; 1Tar 17.1-14 Sarki Dawuda fa ya miƙe tsaye, ya ce, “Ku saurare ni, ku 'yan'uwana, da jama'ata. Na yi niyya a zuciyata in gina wa akwatin alkawari na Ubangiji wurin hutawa, da wurin zaman zatin Allah. Na riga na yi shiri domin ginin, 3amma Allah bai yardar mini in yi da kaina ba, domin ni mayaƙi ne, na kuwa zubar da jini. 4Duk da haka Ubangiji Allah na Isra'ila ya zaɓe ni da zuriyata daga cikin gidan mahaifina, in zama Sarkin Isra'ilawa har abada. Gama shi ya zaɓi Yahuza ya zama shugaba. Daga cikin gidan Yahuza kakana, da kuma daga cikin 'ya'yan mahaifina, maza, ya ji daɗina har ya naɗa ni sarkin dukan Isra'ila. 5Daga cikin dukan 'ya'yana maza, (gama Ubangiji ya ba ni 'ya'ya maza da yawa), ya zaɓi ɗana Sulemanu ya hau gadon sarautar Isra'ila, abin mulkin Ubangiji.
6“Ya ce mini, ‘Ɗanka Sulemanu ne zai gina Haikalina da shirayuna, gama na zaɓe shi ya zama ɗa a gare ni, ni kuwa in zama uba a gare shi. 7Zan tabbatar da mulkinsa har abada idan ya bi umarnaina da ka'idodina da himma kamar yadda ake yi a yau.’
8“Saboda haka a gaban dukan Isra'ila, wato taron jama'ar Ubangiji, da kuma gaban Allahnmu, sai ku kiyaye, ku bi dukan umarnan Ubangiji Allahnku don ku mallaki ƙasan nan mai kyau, ku kuma bar wa 'ya'yanku ita gādo har abada.
9“Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada. 10Ka lura, gama Ubangiji ya zaɓe ka domin ka gina Haikali, wato Wuri Mai Tsarki. Ka yi ƙarfi, ka kama aiki.”
11Sa'an nan Dawuda ya ba ɗansa Sulemanu tsarin shirayin Haikalin, da ɗakunansa, da ɗakunan ajiya, da benaye, da Wuri Mafi Tsarki, inda ake gafarta zunubi. 12Ya kuma ba shi tsarin dukan abin da ya yi nufin yi, na filayen Haikalin Ubangiji da dukan ɗakuna na kewaye, da ɗakunan ajiya na Haikalin Allah, da ɗakunan ajiye kyautan da aka keɓe ga Ubangiji. 13Ya kuma ba shi tsarin ƙungiyoyin firistoci da na Lawiyawa, da na dukan hidimar da za a yi a Haikalin Ubangiji, da aikin lura da kayayyakin aiki na cikin Haikalin Ubangiji. 14Ya kuma faɗa wa Sulemanu yawan zinariya da za a yi kwanoni da ita don yin aiki, da yawan azurfa da za a yi kwanoni da ita don yin aiki, 15da yawan zinariya da za a yi alkukan fitilu, da kuma fitilun, da yawan zinariya da za a yi kowane alkuki da fitilunsa, da yawan azurfa da za a yi alkuki bisa ga yadda za a yi amfani da kowane alkuki, 16da yawan zinariya da za a yi teburorin gurasar ajiyewa, da azurfar da za a yi teburorin azurfa, 17da yawan zinariya tsantsa wadda za a yi cokula masu yatsotsi, da daruna, da finjalai, da kwanoni da ita, da yawan azurfa da za a yi kwanoni da ita, 18da yawan zinariya tsantsa wadda za a yi bagaden ƙona turare da ita. Ya kuma ba shi tsarin zinariya ta kerubobin da za su miƙe fikafikansu su rufe akwatin alkawari na Ubangiji. 19Sarki Dawuda ya ce, “Dukan wannan rubutacce ne daga wurin Ubangiji zuwa gare ni domin in fahimci fasalin aikin filla filla.”
20Sarki Dawuda kuma ya ce wa ɗansa Sulemanu, “Ka yi ƙarfin hali, ka dāge sosai, ka kama aikin, kada ka ji tsoro, kada kuwa ka karai, gama Ubangiji Allah, wato Allahna, yana tare da kai. Ba zai bari ka ji kunya ba, ba kuwa zai rabu da kai ba, har ka gama dukan aikin Haikalin. 21Ga dai ƙungiyoyin firistoci da na Lawiyawa, suna nan domin yin hidima a Haikalin Allah, ga kuma gwanaye na kowace irin sana'a suna tare da kai don yin kowane irin aiki. Shugabanni da dukan jama'a suna ƙarƙashinka duka.”

Currently Selected:

1Tar 28: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in