1Tar 22
22
1Sa'an nan sai Dawuda ya ce, “A nan Haikalin Ubangiji Allah zai kasance, da kuma bagaden ƙona hadaya domin Isra'ila.”
Shirye-shiryen da Dawuda Ya Yi domin Gina Haikali
2Dawuda kuwa ya umarta a tattaro dukan baƙin da suke a ƙasar Isra'ila. Ya sa waɗansu su farfasa duwatsu, su sassaƙe duwatsun domin ginin Haikalin Allah. 3Dawuda kuma ya cika manyan ɗakunan ajiya da ƙarafa don yin ƙusoshi na ƙyamaren ƙofofi, da mahaɗai, ya kuma tara tagulla mai yawa wanda ta fi ƙarfin awo, 4da katakan al'ul da ba a san adadinsu ba, gama Sidoniyawa da mutanen Taya sun kawo wa Dawuda itacen al'ul mai ɗumbun yawa. 5Dawuda kuwa ya ce, “Ɗana Sulemanu yaro ne, bai gogu da duniya ba. Ga shi, Haikalin da za a gina wa Ubangiji zai zama mai ƙayatarwa ƙwarai, zai zama sananne mai daraja cikin dukan ƙasashe, saboda haka sai in tanada masa.” Domin haka Dawuda ya tara kayayyakin gini masu ɗumbun yawa kafin rasuwarsa.
6Sai Dawuda ya kira Sulemanu ɗansa, ya yi masa wasiyyar gina Haikalin Ubangiji, Allah na Isra'ila. 7#2Sam 7.1-16; 1Tar 17.1-14 Dawuda kuwa ya ce wa Sulemanu, “Ɗana, na ƙudura a zuciyata in gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allah. 8Amma Ubangiji ya ce mini, ‘Ka zubar da jini da yawa, ka yi manyan yaƙe-yaƙe, don haka ba za ka gina Haikali saboda sunana ba, gama a gabana ka zubar da jini mai yawa a duniya. 9Za a haifa maka ɗa, zai zama mutumin salama. Zan kuwa ba shi zaman lafiya da abokan gāba da suke kewaye da shi, gama za a ce da shi Sulemanu, wato salama. Zan kawo wa Isra'ila salama, da natsuwa a zamaninsa. 10Shi zai gina Haikali saboda sunana. Zai zama ɗana, ni kuwa zan zama uba a gare shi, zan kafa gadon sarautarsa a Isra'ila har abada.’
11“To, ɗana, Ubangiji ya kasance tare da kai, domin ka yi nasara ka gina Haikalin Ubangiji Allahnka, kamar yadda ya faɗa a kanka. 12Ubangiji dai ya ba ka basira da haziƙanci domin sa'ad da ya sa ka ka lura da Isra'ila ka kiyaye dokokinsa. 13#Josh 1.6-9 Za ka arzuta idan ka kula ka kiyaye dokoki da ka'idodi da Ubangiji ya umarci Musa saboda Isra'ila. Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karaya. 14Da wahala mai yawa na yi tanadi domin Haikalin Ubangiji, zinariya wajen talanti dubu ɗari (100,000), da azurfa kuma wajen talanti zambar dubu (1,000,000), domin gina Haikalin Ubangiji. Bayan wannan akwai tagulla da ƙarfe masu tarin yawa. Na kuma tanada katakai da duwatsu. Kai kuma sai ka ƙara a kansu. 15Kana da ma'aikata jingim, su masu fasa duwatsu, da magina, da masassaƙa, da gwanayen masu sana'o'i iri dabam dabam, masu yawan gaske. 16Za su yi aiki da zinariya, da azurfa, da tagulla, da ƙarfe. Tashi, ka kama aiki, Ubangiji ya kasance tare da kai!”
17Dawuda kuma ya umarci dukan shugabannin Isra'ila su taimaki ɗansa Sulemanu. 18Ya ce, “Ubangiji Allahnku yana tare da ku, ya ba ku zaman lafiya a kowane sashi. Gama ya ba da mazaunan ƙasar a hannuna, an murƙushe ƙasar a gaban Ubangiji da jama'arsa. 19Yanzu fa sai ku sa hankalinku da zuciyarku ga neman Ubangiji Allahnku. Ku tashi, ku gina wa Ubangiji Allah tsattsarkan wuri domin a kawo akwatin alkawari na Ubangiji, da tsarkakakkun tasoshin Allah a cikin Haikalin da aka gina saboda sunan Ubangiji.”
Currently Selected:
1Tar 22: HAU
Highlight
Share
Compare
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979