YouVersion Logo
Search Icon

Romawa Gabatarwa

Gabatarwa
Gabatarwa
Wasiƙa zuwa ga Romawa doguwar wasiƙa ce ta hannun manzon Bulus zuwa ga ikkilisiyar Roma, wadda ta ƙunshi Kirista Al’ummai da kuma Yahudawa. A lokacin rubutun wannan wasiƙa, Bulus yana shirin yă ziyarci Roma ne. Manufar Bulus ta rubuta wannan shi ne don yă gabatar da kansa da kuma koyarwarsa game da labarin nan mai daɗi na Yesu zuwa ga ikkilisiyar Roma yă kuma nemi taimakonsu don shirin aikin wa’azinsa a Sifen. Cikin rubutu zuwa ga mutanen da bai taɓa saduwa da su ba, Bulus ya ba da cikakken bayanin koyarwarsa game da Kiristi, ceto, bangaskiya, dangantaka tsakanin Yahudawa da Al’ummai, dangantaka tsakanin Kirista da hukumomin duniya, da kuma yin sabuwar rayuwa zaunanne cikin ƙaunar Kirista.

Currently Selected:

Romawa Gabatarwa: SRK

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in