Romawa 3:25-26
Romawa 3:25-26 SRK
Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba ya yi haka domin yă nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda yă zama mai adalci da mai kuɓutar da waɗanda suke ba da gaskiya a cikin Yesu.






