Filibbiyawa Gabatarwa
Gabatarwa
Gabatarwa
Manzo Bulus ya rubuta wannan Wasiƙar Bulus zuwa ga Filibbiyawa a tsakanin shekara ta 59 da shekara ta 61 bhy. Filibbi wani muhimmin birni ne a tsohuwar Giris da yake a tsakiya muhimmiyar hanya tsakanin yammancin Asiya Ƙarama da Roma. Bulus ya taimaka kafa ikkilisiya a nan kuma wasiƙar tana da abubuwa masu yawa da wasiƙar abokantaka takan ƙunsa, tana nuna cewa Bulus ya kasance da soyayya mai girma wa al’ummar masu bi. Mai yiwuwa an rubuta wasiƙar daga kurkuku a Roma, Kaisariya, ko Afisa. Bulus ya gode wa Filibbiyawa saboda addu’arsu da kuma kyautansu, ya kuma yi amfani da waƙa mai kyau don yă koya musu game da sauƙinkai na gaskiya, yă gargaɗe su game da koyarwar ƙarya, yă ƙarfafa su cikin bangaskiyarsu ga Kiristi, yă kuma bayyana musu yadda Allah ya ƙarfafa shi tun sa’ad da Romawa suka kama shi.
Currently Selected:
Filibbiyawa Gabatarwa: SRK
Highlight
Share
Copy

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.