Filibbiyawa 2:3-8
Filibbiyawa 2:3-8 SRK
Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku. Bai kamata kowannenku yă kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai yă kula da sha’anin waɗansu ma. A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu. Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake, bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba, amma ya mai da kansa ba kome ba, yana ɗaukan ainihin surar bawa, aka yi shi cikin siffar mutum. Aka kuma same shi a kamannin mutum, ya ƙasƙantar da kansa ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa, mutuwar ma ta gicciye!