Mattiyu Gabatarwa
SRK
Gabatarwa
Da farkon fari, Mattiyu ya gabatar da Yesu a matsayin Almasihu wanda ya cika Nassosin Yahudawa. Waɗansu masana sun kira Mattiyu “mafi Yahudanci” na Bisharu. An gabatar da koyarwar Yesu a jawabai guda biyar. Hanyar da za a shirya koyarwar Yesu sun sa masu karatu na Yahudawa suka tuna da Musa, domin alʼadunsu sun koyar cewa Musa ya rubuta littattafai biyar na Doka (Attaura). Wannan kamanni ya ba da raʼayin cewa marubucin Mattiyu yana gabatar da Yesu a matsayin “sabon Musa.” Littafin kuma ya ci gaba da ambatar Nassosin Yahudawa, yana amfani da salon rubutun Yahudawa, yana kuma ɗaukan alamun da Yahudawa suka saba da su a lokacin. Masana kuma suna kira Mattiyu “Bisharar ikkilisiya”, saboda littafin ya mai da hankali a kan Yesu a matsayin Ubangiji wanda ya tashi daga matattu, a kan mulkin sama, da kuma a kan ikkilisiya kanta. Hakika, Mattiyu ne Bishara kaɗai da ta yi amfani da kalmar Girik na “ikkilisiya.” Sau da dama Mattiyu yakan nuna Yesu tsaye “waje da lokaci,” yana gabatar da ayyukan Yesu a yanayi da kuma cikin tarihi da kuma ɗaukakarsa a matsayin madawwami, Ubangiji da ya tashi daga matattu.

Hausa New Testament (Nigeria) ©2009, 2013 Biblica, Inc. All rights reserved worldwide.

Learn More About Sabon Rai Don Kowa