YouVersion Logo
Search Icon

Irmiya 9

9
1Da ma kaina maɓulɓulan ruwa ne
idanuna kuma maɓulɓulan hawaye!
Da sai in yi kuka dare da rana
saboda mutanena da aka kashe.
2Da ma a hamada
ina da wurin da matafiye za su sauka,
don in bar mutanena
in tafi in bar su;
gama dukansu mazinata ne,
taron mutane marasa aminci.
3“Sun tanƙwasa harshensu
kamar baka, don su harba ƙarya;
ba da gaskiya ba ne
suke nasara a cikin ƙasar.
Sukan tashi daga wannan zunubi zuwa wancan;
ba su san ni ba,”
in ji Ubangiji.
4“Ka yi hankali da abokanka;
kada ka amince da ’yan’uwanka.
Gama kowane ɗan’uwa munafuki ne,
kowane aboki kuma mai kushe ne.
5Aboki kan ruɗi aboki,
ba mai faɗar gaskiya.
Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya;
sun gajiyar da kansu da yin zunubi.
6Kai#9.6 Wato, Irmiya (jam’i na mutum guda a Ibraniyanci) kana zama a tsakiyar ruɗu;
cikin ruɗunsu sun ƙi su san ni,”
in ji Ubangiji.
7Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,
“Ga shi zan tace in kuma gwada su,
gama me kuwa zan yi
saboda zunubin mutanena?
8Harshensu kibiya ce mai dafi;
yana magana da ruɗu.
Da bakinsa kowa yana maganar alheri da maƙwabcinsa,
amma a zuciyarsa ya sa masa tarko.
9Bai kamata in hukunta su saboda wannan ba?”
In ji Ubangiji.
“Bai kamata in ɗau fansa
a kan irin al’umma kamar wannan ba?”
10Zan yi kuka in yi kururuwa saboda duwatsu
in kuma yi makoki game da wuraren kiwon hamada.
Sun zama kango ba wanda yake bi cikinta,
ba a kuma jin kukan shanu.
Tsuntsaye sararin sama sun gudu
namun jeji ma duk sun watse.
11“Zan mai da Urushalima tsibin kufai,
wurin zaman diloli;
zan kuma lalace garuruwan Yahuda
saboda haka ba wanda zai zauna a can.”
12Wane mutum ne yana da isashiyar hikimar fahimtar wannan? Wa Ubangiji ya umarta da zai iya yin bayani? Me ya sa aka lalace ƙasar ta zama kufai kamar hamada da ba wanda zai iya ratsa ta?
13 Ubangiji ya ce, “Domin sun bar dokata, wadda na sa a gabansu; ba su yi biyayya da ni ko su bi dokata ba. 14A maimako, sun bi taurin zuciyarsu; suka bi Ba’al, yadda kakanninsu suka koya musu.” 15Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Ga shi zan sa wannan mutane su ci abinci mai ɗaci su kuma sha ruwan dafi. 16Zan watsar da su a cikin al’ummai da su da kakanninsu ba su sani ba, zan kuma fafare su da takobi sai na hallaka su.”
17Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,
“Ku lura yanzu! Ku kira mata masu makoki su zo
ku aika wa gwanaye a cikinsu su zo.
18Bari su zo da sauri
su yi kuka a kanmu
sai idanunmu sun cika da hawaye
giranmu kuma su jiƙe sharkaf.
19An ji karar kuka daga Sihiyona cewa,
‘Duba yadda muka lalace!
Duba irin babban kunyar da muka sha!
Dole mu bar ƙasar
domin gidajenmu sun lalace.’ ”
20Yanzu, ya mata, ku ji maganar Ubangiji;
ku buɗe kunnuwanku ga maganar bakina.
Ku koya wa ’yan matanku yadda za su yi kuka;
ku koya wa juna makoki.
21Mutuwa ta haura ta tagoginmu
ta kuma shiga katangarmu;
ta karkashe ’ya’ya a tituna
ta kuma karkashe samari a dandali.
22Ka ce, “Ga abin da Ubangiji ya furta,
“ ‘Gawawwakin mutane za su fāɗi
kamar juji a fili,
kamar hatsin da aka yanka a bayan mai girbi,
da ba mai tara su.’ ”
23Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa
ko mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa
ko mai arziki ya yi fariya da arzikinsa,
24amma bari shi wanda yake taƙama ya yi taƙama da wannan,
cewa ya fahimci ya kuma san ni,
cewa ni ne Ubangiji, wanda yake yin alheri,
gaskiya da kuma adalci a duniya,
gama a waɗannan ne nake jin daɗi,”
in ji Ubangiji.
25“Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan hukunta dukan waɗanda aka yi musu kaciya kawai a jiki, 26Masar, Yahuda, Edom, Ammon, Mowab da dukan waɗanda suke zaune a hamada a wurare masu nisa.#9.26 Ko kuwa hamada da kuma waɗanda suke hawan gashi kai ta goshinsu Gama dukan waɗannan al’ummai marasa kaciya ne, har dukan gidan Isra’ila ma marasa kaciya ne a zuciya.”

Currently Selected:

Irmiya 9: SRK

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in