YouVersion Logo
Search Icon

2 Sarakuna 2

2
An ɗauki Iliya zuwa sama
1Da lokaci ya yi da Ubangiji zai ɗauki Iliya zuwa sama cikin guguwa, Iliya da Elisha kuwa suna kan hanyarsu daga Gilgal. 2Sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ka dakata a nan; Ubangiji ya aike ni Betel.”
Amma Elisha ya amsa ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai kuma kana a raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka gangara zuwa Betel.
3Sai ƙungiyar annabawa a Betel suka fito zuwa wajen Elisha suka ce masa, “Ka san cewa Ubangiji zai ɗauki maigidanka daga wurinka yau?”
Sai ya ce, “I, na sani, amma kada ku yi magana game da wannan.”
4Sai Iliya ya ce masa, “Ka dakata a nan Elisha; Ubangiji ya aike ni Yeriko.”
Sai ya ce masa, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai ma kana a raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka sai suka tafi Yeriko.
5Ƙungiyar annabawa a Yeriko suka haura zuwa wajen Elisha suka ce, “Ko ka san Ubangiji zai ɗauki maigidanka daga gare ka yau?”
Sai ya ce, “I, na sani, amma ku bar zancen nan tukuna.”
6Sai Iliya ya ce masa, “Ka dakata a nan, Ubangiji ya aike ni Urdun.”
Sai Elisha ya ce masa, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai kuma kana raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka ci gaba da tafiya tare.
7Mutum hamsin na ƙungiyar annabawa suka je suka tsaya da nisa, suna fuskantar inda Iliya da Elisha suka tsaya a Urdun. 8Sai Iliya ya tuɓe rigarsa, ya nannaɗe ya bugi ruwan Urdun da shi. Sai ruwan ya dāre gida biyu, suka haye a busasshiyar ƙasa.
9Da suka haye, sai Iliya ya ce wa Elisha, “Faɗi mini, abin da kake so in yi maka kafin a ɗauke ni daga gare ka!”
Elisha ya amsa ya ce, “Bari in gāji ninki biyu na ruhunka.”
10Iliya ya ce, “Ka nemi abu mai wuya, amma in ka ga lokacin da aka ɗauke ni daga gare ka, zai zama naka, in ba haka ba, ba za ka samu ba ke nan.”
11Yayinda suke tafiya suna magana, sai kwatsam, keken yaƙin wuta da dawakan wuta suka ratse tsakaninsu, sai Iliya ya tafi sama a cikin guguwa. 12Da Elisha ya ga haka sai ya yi ihu yana cewa, “Babana! Babana! Kekunan yaƙin da mahayan dawakan Isra’ila!” Elisha kuwa bai sāke ganinsa ba. Sai ya kama tufafinsa ya yayyage.
13Sai ya ɗauki rigar da ta fāɗo daga Iliya ya koma ya tsaya a gaɓar Kogin Urdun. 14Sa’an nan Elisha ya ɗauki rigar da ta fāɗo daga Iliya ya bugi ruwan da shi. Ya ce, “Yanzu ina Ubangiji Allah na Iliya?” Da ya bugi ruwan sai ruwan ya dāre gida biyu, sai ya haye.
15Ƙungiyar annabawa daga Yeriko, waɗanda suke kallo, suka ce, “Ruhun Iliya yana a kan Elisha.” Sai suka je su tarye shi, suka rusuna har ƙasa a gabansa. 16Suka ce, “Duba, mu bayinka muna da masu ji da ƙarfi hamsin. Bari su je su nemi maigidanka. Wataƙila, Ruhun Ubangiji ya ɗauke shi ya ajiye bisa wani dutse, ko wani kwari.”
Elisha ya ce, “A’a, kada ku aike su.”
17Amma suka matsa masa har ya ji ba ya iya hana su. Saboda haka ya ce, “Ku aike su.” Sai suka aiki mutane hamsin, suka yi ta nema har kwana uku amma ba su same Iliya ba. 18Da suka dawo wurin Elisha, wanda yake a Yeriko, sai ya ce musu, “Ban ce muku kada ku tafi ba?”
Ruwan warkarwa
19Mutane garin suka ce wa Elisha, “Ranka yă daɗe, duba, garin yana da kyan gani, amma ruwan ba shi da kyau, ƙasar kuma ba ta ba da amfani.”
20Sai ya ce, “Ku kawo mini sabuwar ƙwarya, ku kuma sa gishiri a ciki.” Sai suka kawo masa.
21Sai ya tafi maɓulɓular ruwan yana watsa gishirin a ciki, yana cewa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Na warkar da ruwan nan. Ba zai ƙara jawo mutuwa, ko yă hana ƙasar ba da amfani ba.’ ” 22Ruwan ya tsabtacce har yă zuwa yau, bisa ga faɗin Elisha.
An yi wa Elisha dariya
23Daga nan sai Elisha ya tafi Betel. Yayinda yake tafiya a hanya, sai waɗansu matasa suka fito daga cikin gari, suka yi masa dariya suna cewa, “Ka haura, ya kai mai kai marar gashi! Ka haura, kai mai kai marar gashi!” 24Sai ya juya ya dube su, ya la’anta su da sunan Ubangiji. Sai beyar guda biyu suka fito daga jeji suka hallaka matasa arba’in da biyu daga cikinsu. 25Sai ya ci gaba zuwa Dutsen Karmel, daga can kuma ya koma Samariya.

Currently Selected:

2 Sarakuna 2: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in