1
Rom 7:25
Littafi Mai Tsarki
HAU
Godiya tā tabbata ga Allah, akwai, ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu! Ashe kuwa, ni a kaina, da hankalina, hakika Shari'ar Allah nake bauta wa, amma da jikina ka'idar zunubi nake bauta wa.
Compare
Explore Rom 7:25
2
Rom 7:18
Don na sani ba wani abin kirki da ya zaune mini, wato a jikina. Niyyar yin abin da yake daidai kam, ina da ita, sai dai ikon zartarwar ne babu.
Explore Rom 7:18
3
Rom 7:19
Nagarin abin da nake niyya yi kuwa, ba shi nake yi ba, sai dai mugun abin da ba na niyya, shi nake aikatawa.
Explore Rom 7:19
4
Rom 7:20
To, idan abin da ba na niyya shi nake yi, ashe kuwa, ba ni nake yinsa ba ke nan, zunubin da ya zaune mini ne.
Explore Rom 7:20
5
Rom 7:21-22
Sai na ga, ashe, ya zama mini ka'ida, in na so yin abin da yake daidai, sai in ga mugunta tare da ni. Ni kam, a birnin zuciyata, na amince da shari'ar Allah.
Explore Rom 7:21-22
6
Rom 7:16
To, idan abin da ba na niyya, shi nake yi, na yarda ke nan Shari'a aba ce mai kyau.
Explore Rom 7:16
Home
Bible
Plans
Videos