1
Rom 6:23
Littafi Mai Tsarki
HAU
Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawwami a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.
Compare
Explore Rom 6:23
2
Rom 6:14
Domin zunubi ba zai mallake ku ba, tun da yake ba shari'a take iko da ku ba alherin Allah ne.
Explore Rom 6:14
3
Rom 6:4
Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka ta da Almasihu daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa.
Explore Rom 6:4
4
Rom 6:13
Kada kuma ku miƙa gaɓoɓinku su zama kayan aikin mugunta, don yin zunubi. Amma ku miƙa kanku ga Allah, kamar waɗanda aka raya bayan mutuwa, kuna miƙa gaɓoɓinku ga Allah kayan aikin adalci.
Explore Rom 6:13
5
Rom 6:6
Wato, mun sani an gicciye halayenmu na dā tare da shi, domin a hallakar da ikon nan namu mai zunnubi, kada mu ƙara bauta wa zunubi.
Explore Rom 6:6
6
Rom 6:11
Haka ku ma sai ku lasafta kanku kamar ku matattu ne ga zunubi, amma kuna a raye rayuwa ga Allah, ta wurin Almasihu Yesu.
Explore Rom 6:11
7
Rom 6:1-2
To, me kuma za mu ce? Ma ci gaba da yin zunubi ne domin alherin Allah yă haɓaka? A'a, ko kusa! Mu da muka mutu ga zunubi, ƙaƙa za mu ƙara rayuwa a cikinsa har yanzu?
Explore Rom 6:1-2
8
Rom 6:16
Ba ku sani ba, shi wanda kuke miƙa kanku a gare shi domin yi wa biyayya, lalle ku bayi ne na wanda kuke yi wa biyayya ɗin (ko bautar zunubi wanda ƙarshensa mutuwa ne, ko bautar biyayya wadda ƙarshenta adalci ce)?
Explore Rom 6:16
9
Rom 6:17-18
Amma godiya tā tabbata ga Allah, ko da yake dā can ku bayin zunubi ne, a yanzu kam kuna biyayya da zuciya ɗaya ga irin koyarwar nan da aka yi muku. Da aka 'yanta ku kuma daga bautar zunubi, kun zama bayin aikin adalci.
Explore Rom 6:17-18
Home
Bible
Plans
Videos