1
Rom 3:23-24
Littafi Mai Tsarki
HAU
gama 'yan adam duka sun yi zunubi, sun kasa kuma ga ɗaukakar Allah. Amma ta wurin alherin da Allah ya yi musu kyauta, sun sami kuɓuta ta wurin fansar da Almasihu Yesu ya yi.
Compare
Explore Rom 3:23-24
2
Rom 3:22
Adalcin nan na Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya ga Yesu Almasihu, na masu ba da gaskiya ne dukka, ba kuwa wani bambamci
Explore Rom 3:22
3
Rom 3:25-26
Allah kuwa ya ayyana Yesu Almasihu ya zama hadayar sulhu, ta wurin ba da gaskiya ga jininsa. Allah kuwa ya yi haka domin yă nuna adalcinsa ne, domin dā saboda haƙurinsa ya jingine zunuban da aka gabatar, domin a nuna adalcinsa a wannan zamani, wato a bayyana shi kansa mai adalci ne, mai kuɓutar da duk mai gaskatawa da Yesu kuma.
Explore Rom 3:25-26
4
Rom 3:20
Ai, ba wani ɗan adam da zai sami kuɓuta ga Allah ta kiyaye ayyukan Shari'a, tun da yake ta Shari'a ne mutum yake ganin laifinsa.
Explore Rom 3:20
5
Rom 3:10-12
Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Babu wani mai adalci, babu, ko ɗaya, Babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah. Duk sun bauɗe, sun zama marasa amfani baki ɗaya, Babu wani mai aiki nagari, babu kam, ko da guda ɗaya.”
Explore Rom 3:10-12
6
Rom 3:28
Domin mun amince, cewa ta bangaskiya ne mutum yake kuɓuta, ba ta kiyaye ayyukan Shari'a ba.
Explore Rom 3:28
7
Rom 3:4
A'a, ko kusa! A dai tabbata Allah mai gaskiya ne, ko da yake kowane mutum maƙaryaci ne, yadda yake a rubuce cewa, “Don maganarka tă tabbatar da adalcinka, Ka kuma yi rinjaye in an binciki al'amarinka.”
Explore Rom 3:4
Home
Bible
Plans
Videos