1
Rom 15:13
Littafi Mai Tsarki
HAU
Allah mai kawo sa zuciya, yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama saboda bangaskiyarku, domin ku yi matuƙar sa zuciya ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
Compare
Explore Rom 15:13
2
Rom 15:4
Ai, duk abin da aka rubuta tun dā, an rubuta shi ne domin a koya mana, domin mu ɗore a cikin sa zuciyar nan tamu ta wurin haƙuri da ta'aziyyar da Littattafai suke yi mana.
Explore Rom 15:4
3
Rom 15:5-6
Allah mai ba da haƙuri da ta'aziyya, yă ba ku zaman lafiya da juna bisa halin Almasihu Yesu, domin ku ɗaukaka Allah, Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma Ubansa, nufinku ɗaya, bakinku ɗaya.
Explore Rom 15:5-6
4
Rom 15:7
Saboda haka ku karɓi juna da hannu biyu biyu, kamar yadda Almasihu ya karɓe ku hannu biyu biyu, domin a ɗaukaka Allah.
Explore Rom 15:7
5
Rom 15:2
Kowannenmu yă faranta wa maƙwabcinsa rai, don kyautata zamansa da kuma inganta shi.
Explore Rom 15:2
Home
Bible
Plans
Videos