1
Rom 12:2
Littafi Mai Tsarki
HAU
Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.
Compare
Explore Rom 12:2
2
Rom 12:1
Don haka ina roƙonku 'yan'uwa, saboda yawan jinƙai na Allah, ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi.
Explore Rom 12:1
3
Rom 12:12
Sa zuciyar nan taku ta sa ku farin ciki, ku jure wa wahala, ku nace wa yin addu'a.
Explore Rom 12:12
4
Rom 12:21
Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.
Explore Rom 12:21
5
Rom 12:10
A game da ƙaunar 'yan'uwa kuwa, ku ƙaunaci juna gaya. A wajen ba da girma, kowa yă riga ba ɗan'uwansa.
Explore Rom 12:10
6
Rom 12:9
Ƙauna ta kasance sahihiya. Ku yi ƙyamar abin da yake mugu, ku lazamci abin da yake nagari.
Explore Rom 12:9
7
Rom 12:18
In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa.
Explore Rom 12:18
8
Rom 12:19
Ya ku ƙaunatattuna, kada ku ku yi ramuwa, sai dai ku bar wa fushin Allah. Domin a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce, ni zan saka, in ji Ubangiji.”
Explore Rom 12:19
9
Rom 12:11
Kada ku sassauta a wajen himma, ku himmantu a ruhu, kuna bauta wa Ubangiji.
Explore Rom 12:11
10
Rom 12:3
Albarkacin alherin da aka yi mini ina yi wa kowannenku gargaɗi kada ya ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, sai dai ya san kansa, gwargwadon bangaskiyar da Allah ya ba shi.
Explore Rom 12:3
11
Rom 12:17
Kada ku rama muguntar kowa da mugunta. Ku yi ta lura al'amuranku su zama daidai a gaban kowa.
Explore Rom 12:17
12
Rom 12:16
Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna alfarma, sai dai ku miƙa kanku ga aikata ayyukan tawali'u. Kada ku aza kanku masu hikima ne.
Explore Rom 12:16
13
Rom 12:20
Har ma “in maƙiyinka yana jin yunwa, sai ka ci da shi. In yana jin ƙishirwa, ka shayar da shi. Don ta haka ne za ka tula garwashin wuta a kansa.”
Explore Rom 12:20
14
Rom 12:14-15
Ku sa wa masu tsananta muku albarka. Ku sa musu albarka, kada ku la'ance su. Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka.
Explore Rom 12:14-15
15
Rom 12:13
Ku agaji tsarkaka, ku himmantu ga yi wa baƙi alheri.
Explore Rom 12:13
16
Rom 12:4-5
Wato kamar yadda gaɓoɓi da yawa suke harhaɗe a jiki ɗaya, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba, haka mu ma, ko da yake muna da yawa, jiki ɗaya muke haɗe da Almasihu, kowannenmu kuma gaɓar ɗan'uwansa ne.
Explore Rom 12:4-5
Home
Bible
Plans
Videos