1
Zab 63:1
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ya Allah, kai ne Allahna, Ina sa zuciya gare ka. Duk niyyata ta nemanka ce, Raina yana ƙishinka, Kamar bussasshiyar ƙasa, Wadda ta zozaye, ba ta da ruwa.
Compare
Explore Zab 63:1
2
Zab 63:3
Madawwamiyar ƙaunarka ta fi rai kansa, Saboda wannan zan yabe ka.
Explore Zab 63:3
3
Zab 63:4
Muddin raina, zan yi maka godiya, Zan ta da hannuwana sama, in yi addu'a gare ka.
Explore Zab 63:4
4
Zab 63:2
Bari in gan ka a tsattsarkan wurinka, In dubi ɗaukakarka da darajarka.
Explore Zab 63:2
5
Zab 63:7-8
Domin kai kake taimakona kullayaumin. Da murna, nake raira waƙa, A inuwar fikafikanka, Raina yana manne maka, Ikonka yana riƙe da ni.
Explore Zab 63:7-8
6
Zab 63:6
Sa'ad da nake kwance a gadona na tuna da kai, Dare farai ina ta tunawa da kai
Explore Zab 63:6