1
K.Mag 4:23
Littafi Mai Tsarki
HAU
Tunane-tunanenka mafarin rai ne kansa, ka kiyaye su abin mallakarka ne mafi daraja.
Compare
Explore K.Mag 4:23
2
K.Mag 4:26
Ka tabbata ka san abin da kake yi, duk abin da kake yi kuma zai zama daidai.
Explore K.Mag 4:26
3
K.Mag 4:24
Kada ka faɗi kowane abu da yake ba na gaskiya ba, kada wani abu ya haɗa ka da ƙarya, ko maganganun ruɗawa.
Explore K.Mag 4:24
4
K.Mag 4:7
Samun hikima shi ne mafificin abin da za ka yi. Kome za ka samu dai, ka sami basira.
Explore K.Mag 4:7
5
K.Mag 4:18-19
Hanyar da adalai suke bi kamar fitowar rana ce, sai ta yi ta ƙara haske, har ta take tsaka. Hanyar mugaye kuwa duhu ne baƙi ƙirin, kamar duhun dare. Sukan fāɗi, amma ba su san abin da ya sa suka yi tuntuɓe ba.
Explore K.Mag 4:18-19
6
K.Mag 4:6
Kada ka rabu da hikima, gama za ta kiyaye ka, ka ƙaunace ta, za ta kiyaye lafiyarka.
Explore K.Mag 4:6
7
K.Mag 4:13
Kullum ka tuna da abin da ka koya, iliminka shi ne ranka, ka lura da shi da kyau.
Explore K.Mag 4:13
8
K.Mag 4:14
Kada ka tafi inda mugaye suke tafiya, kada ka bi gurbin mugaye.
Explore K.Mag 4:14
9
K.Mag 4:1
'Ya'yana ku kasa kunne ga koyarwar mahaifinku. Ku mai da hankali, za ku zama haziƙai.
Explore K.Mag 4:1
Home
Bible
Plans
Videos