1
K.Mag 3:5-6
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ka dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani. A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai.
Compare
Explore K.Mag 3:5-6
2
K.Mag 3:7
Sam, kada ka yarda ka ɗauki kanka kai mai hikima ne fiye da yadda kake, kai dai ka ji tsoron Ubangiji, ka rabu da aikata mugunta.
Explore K.Mag 3:7
3
K.Mag 3:9-10
Ka girmama Ubangiji ta wurin miƙa masa hadaya daga mafi kyau na amfanin gonarka. Idan ka yi haka rumbunanka za su cika da hatsi. Za ka sami ruwan inabi mai yawa, har ka rasa wurin da za ka zuba shi duka.
Explore K.Mag 3:9-10
4
K.Mag 3:3
Kada ka yarda ka rabu da biyayya da aminci, ka ɗaura su a wuyanka, ka rubuta su kuma a zuciyarka.
Explore K.Mag 3:3
5
K.Mag 3:11-12
Ɗana, sa'ad da Ubangiji ya tsauta maka ka mai da hankali sosai, ka kuma yarda da gargaɗinsa. Ubangiji yana tsauta wa waɗanda yake ƙauna. Kamar yadda mahaifi yakan tsauta wa ɗan da yake fāriya da shi.
Explore K.Mag 3:11-12
6
K.Mag 3:1-2
Ɗana kada ka manta da abin da na koya maka. Kullum ka tuna da abin da na faɗa maka ka yi. Koyarwata za ta ba ka tsawon rai da wadata.
Explore K.Mag 3:1-2
7
K.Mag 3:13-15
Mai farin ciki ne mutumin da ya zama mai hikima, ya kuma sami fahimi. Yana da riba mai yawan gaske fiye da ta azurfa, tamaninta a gare ka ya fi na zinariya. Tamanin hikima ya fi na lu'ulu'ai, ya kuma fi kowane irin abin da kake so tamani.
Explore K.Mag 3:13-15
8
K.Mag 3:27
Ka yi wa masu bukata alheri a duk lokacin da kake iyawa.
Explore K.Mag 3:27
9
K.Mag 3:19
Ubangiji ya halicci duniya ta wurin hikimarsa, Ya shimfiɗa sararin sama a inda yake ta wurin saninsa.
Explore K.Mag 3:19
Home
Bible
Plans
Videos