1
L.Ƙid 21:8
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙera maciji da tagulla, ka sarƙafa shi a bisa dirka, duk wanda maciji ya sare shi, idan ya dubi maciji na tagullar, zai rayu.”
Compare
Explore L.Ƙid 21:8
2
L.Ƙid 21:9
Musa kuwa ya yi maciji na tagulla, ya sarƙafa shi a bisa dirka, idan kuwa maciji ya sari mutum, in ya dubi macijin tagullar, zai warke.
Explore L.Ƙid 21:9
3
L.Ƙid 21:5
Suka yi wa Allah gunaguni, da Musa kuma, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu cikin jeji mu mutu? Gama ba abinci, ba ruwa, mu kuwa mun gundura da wannan abinci marar amfani.”
Explore L.Ƙid 21:5
4
L.Ƙid 21:6
Sai Ubangiji ya aiko macizai masu zafin dafi a cikin jama'a, suka sassari Isra'ilawa, da yawa kuwa suka mutu.
Explore L.Ƙid 21:6
5
L.Ƙid 21:7
Jama'a kuwa suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi gama mun yi wa Ubangiji gunaguni, mun kuma yi maka. Ka roƙi Ubangiji ya kawar mana da macizan.” Musa kuwa ya yi roƙo domin jama'ar.
Explore L.Ƙid 21:7