1
Mat 17:20
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ya ce musu, “Saboda ƙarancin bangaskiyarku. Domin hakika ina gaya muku, da kuna da bangaskiya, ko misalin ƙwayar mustad, da za ku ce wa dutsen nan, ‘Kawu daga nan, ka koma can!’, sai kuwa ya kawu. Ba kuwa abin da zai gagare ku.
Compare
Explore Mat 17:20
2
Mat 17:5
Yana magana ke nan sai ga wani gajimare mai haske ya zo ya rufe su. Aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi.”
Explore Mat 17:5
3
Mat 17:17-18
Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku marasa bangaskiya, kangararru na wannan zamani! Har yaushe zan zama da ku? Har yaushe kuma zan jure muku? Ku kawo mini shi nan.” Sai Yesu ya tsawata masa, aljanin kuma ya rabu da shi. Nan take yaron ya warke.
Explore Mat 17:17-18
Home
Bible
Plans
Videos