1
L.Mah 16:20
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Sai ya farka daga barcinsa, ya ce, “Zan fita kamar yadda na saba yi koyaushe, in miƙe jikina.” Ashe, bai sani ba, Ubangiji ya rabu da shi.
Compare
Explore L.Mah 16:20
2
L.Mah 16:28
Sa'an nan Samson ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allah, ka tuna da ni, ina roƙonka, ka ƙarfafa ni sau ɗayan nan kaɗai, don in ɗauki fansa a kan Filistiyawa saboda idona biyu da suka ƙwaƙule mini.”
Explore L.Mah 16:28
3
L.Mah 16:17
A ƙarshe ya faɗa mata ainihin gaskiyar, ya ce mata, “Ba a taɓa aske gashin kaina ba, gama ni keɓaɓɓe ga Ubangiji ne tun daga cikin uwata. Idan aka yi mini aski, to, ƙarfina zai rabu da ni, in zama marar ƙarfi kamar kowa.”
Explore L.Mah 16:17
4
L.Mah 16:16
Sa'ad da ta fitine shi yau da gobe da yawan maganganunta, ta tunzura shi, sai ransa ya ɓaci kamar zai mutu.
Explore L.Mah 16:16
5
L.Mah 16:30
ya yi kuwwa ya ce, “Bari in mutu tare da Filistiyawa!” Ya sunkuya da iyakar ƙarfinsa. Ɗakin kuwa ya faɗa a kan shugabannin da dukan mutanen da suke a cikin ɗakin. Mutanen da Samson ya kashe a rasuwarsa sun fi waɗanda ya kashe sa'ad da yake da rai.
Explore L.Mah 16:30
Home
Bible
Plans
Videos