Tun da farko na faɗa muku yadda abin zai zama,
Tuntuni na yi faɗi a kan abin da zai faru.
Na kuwa ce shirye-shiryena ba za su taɓa fāɗuwa ba,
Zan aikata dukan abin da na yi niyyar yi.
Ina kiran wani mutum ya zo daga gabas,
Zai kawo sura kamar shaho,
Zai kammala abin da na shirya.
Na yi faɗi, zai kuwa cika.